Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin rabawa jami’o’in kasar naira biliyan 22.72 a ranar Laraba
  • Ministan kwadago, Chris Ngige, wanda ya tabbatar da hakan ya ce ma'aikatar kudi da tsare-tsare ta tarayya za ta fara rabon kudaden
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta yi barazanar komawa yajin aiki idan har ba a cika mata alkawaranta ba

Abuja - Ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce ma'aikatar kudi da tsare-tsare ta tarayya za ta fara rabon kudade ga jami'o'i a ranar Laraba, rahoton Premium Times.

Ministan ya ce gwamnati na da tabbacin cewa kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ba za ta tafi yajin aikin da ta shirya zuwa ba.

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari
Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin 'Politics Today' na Channels TV a ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

A ranar Litinin, Victor Osodeke, shugaban kungiyar ASUU ya ce za su tafi wani yajin aikin idan gwamnati ta ci gaba da saba yarjejeniyar 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin aiwatar da yarjejeniyar bayan ta janye yajin aikin watanni tara da ta shiga a watan Disamban 2020.

Mista Ngige ya ce gwamnati ta rigada ta cika alkawarin biyan kason farko a watan Janairu kuma tana shirin biyan wasu alawus-alawus na Naira biliyan 22.72.

Ya ce tuni an riga an tura Naira biliyan 30 na asusun farfado da jami’o’in kasar a cikin asusun hukumar jami’o’i ta kasa, kuma an shirya raba kudaden ga makarantu.

Ngige ya ce:

"An biya abun da aka amince da shi a shekarar bara. Wadannan sune kudaden da suka kai biya. An biya wannan a watannin Janairu da Fabrairu. Wannan shine kaso na biyu da za mu biya, naira biliyan 22.72 na kaso na biyu. Naira miliyan 30 na asusun farfado da jami’o’in kasar ma yana a asusun CBN."

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Ya ce har yanzu kungiyar ba ta sanar da ma’aikatarsa batun shiga yajin aikin ba duk da ya tabbatar da cewa ya kalli taron manema labarai inda ASUU ta bayar da wa’adin.

ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3

A baya mun kawo cewa, kungiyar malaman jami’o’i na Najeriya ta ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya makwanni 3 don cika mata sharuddan da ta gindaya wa gwamnatin, The Nation ta ruwaito.

Ta bayyana wannan kudirin nata ne inda ta ce wajibi ne gwamnatin ta cika mata alkawarran da su ka sa hannu akai tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.

ASUU ta ce in har gwamnatin bata cika sharuddan na ta ba cikin makwanni 3 za ta dauki tsattsauran mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel