Bayan shekaru 5 da ɓatan ɗiyarsa, mahaifi ya rubuta wasiƙa mai taɓa zuciya

Bayan shekaru 5 da ɓatan ɗiyarsa, mahaifi ya rubuta wasiƙa mai taɓa zuciya

  • Umar Suleiman magidanci ne da diyarsa ta bace a shekaru 5 da suka gabata kuma har yanzu babu amon ta balle labarin ta
  • Ya wallafa wasika ga diyarsa a yayin da aka shekara 5 da sace ta, ya bayyana irin kewar ta da yayi kuma bai cire ran sake ganin ta ba
  • Ya yi addu'ar Allah ya taba zuciyar wadanda suka sace ta su sako ta, ko kuma tana hannu Rabbi mai kowa da komai

Batan mutum babu shakka abu ne da ke kunshe da tashin hankali, ballantana karamin yaro wanda bai san komai ba kuma ba ya iya yi wa kansa komai.

Mummunan tashin hankali ne ya samu Umar Suleiman, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumunta na facebook a shekaru 5 da suka gabata, batan diyarsa mai suna Khadija babu shakka ya girgiza shi.

Kara karanta wannan

Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya

Bayan shekaru 5 da ɓatan ɗiyarsa, mahaifi ya rubuta wasiƙa mai taɓa zuciya
Bayan shekaru 5 da ɓatan ɗiyarsa, mahaifi ya rubuta wasiƙa mai taɓa zuciya. Hoto daga Umar Suleiman
Asali: Facebook

A yanzu dai halin da ake ciki, babu amo balle labarin Khadija har bayan shekaru 5 da sace ta.

A jiya Juma'a ne ya wallafa wata wasika mai taba zuciya inda ya ke bayyana halin da ya ke ciki na jimami tare da yi wa diyarsa fatan bayyanarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook:

"Wasika ga diyata da aka sace. Ya ke Khadija, a yau shekaru 5 cif kenan tun bayan sace ki da aka yi. A gaskiya abu ne mai firgitarwa da kaduwa ga iyayen ki amma har yau ba mu cire rai ba ko bayan shekarun nan.
"Mun kasance masu addu'a kan cewa wata rana nan kiusa za ki sake dawowa tare da mu. Na yi kewar hawayen ki, na yi kewar daukan ki idan kina kuka kuma kina cewa " Kace in yi hakuri" kace mun sorry. Kuma idan na fada miki wadannan kalaman, a take hawayen ki ke kafewa.

Kara karanta wannan

N2tr CBN ta rarraba wa masu kananan sana'o'i da kamfanoni a cikin shekara 1, Emefiele

"A gaskiya babu sauki a ta nan bangarenmu, za mu cigaba da addu'ar Allah ya taba zuciyar wadanda suka sace ki kuma su sake ki. Idan kina raye har yanzu, Allah ya tabbatar mana da sake saduwa.
"Idan kuma ba haka ba, na san kina wurin mahaliccin mai duka. Ina kewar ki Khadija ta. Daga mahaifin ki, Umar Suleiman."

'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

A wani labari na daban, yayin da ‘yan bindiga su ka kai farmaki garin Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, sun halaka mafarauci sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 30.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, lamarin ya auku da misalin 2am na Laraba inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun bi sawun ‘yan bindigan don ceto wadanda su ka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel