Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

  • 'Yan bindiga sun halaka wani mafarauci sannan sun yi garkuwa da a kalla mutane 30 a garin Zazzaga dake karamar hukumar Munya a jihar Neja
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a jihar ta Niger
  • Lamarin ya auku da misalin karfe 2 na daren Laraba kuma ‘yan sanda sun bi sawun ‘yan bindigan domin ceto jama’a

Niger - Yayin da ‘yan bindiga su ka kai farmaki garin Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja, sun halaka mafarauci sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 30.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta wallafa.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger
Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger
Asali: Original

A cewarsa, lamarin ya auku da misalin 2am na Laraba inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun bi sawun ‘yan bindigan don ceto wadanda su ka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata

Sai dai, Sakataren karamar hukumar Munya, James Jagaba, ya sanar da wakilin Daily Trust ta wayar salula ya ce an yi garkuwa da mutane 68, har da mata da yara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sun zo da yawansu yayin da jama’a ke bacci sannan suka fara yadda suka ga dama a garin. Sun halaka mutum daya, sun harbe mutane 3 sannan sun yi garkuwa da mutane 68,” a cewarsa.

Wata majiya daga garin ta ce ‘yan bindigan sun dinga bi gida-gida ne.

“Sun halaka mafaraucin yayin da yake musayar wuta da su. Ba mu san inda suka nufa da wadanda su ka yi garkuwa da su ba. Sai dai jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda, sojoji da ‘yan sa kai sun kewaye garin,”A cewarsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, rashin tsaron kasar nan yana ci gaba da yawa duk da yadda jami’an tsaro suke ta kwantar wa mutane da hankali.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun halaka rayuka 9 tare da sace shanu

A ranar Litinin, Sakataren gwamnatin jihar Najeriya ya bayyana yadda ‘yan Boko Haram suka kwace garuruwa 5 da ke karkashin karamar hukumar Shiroro.

Tsagerun yan bindiga sun sake kai harin Tegina, sun yi awon gaba da ma'aikatan ruwa

A wani labari na daban, Dailytrust ta ruwaito cewa aƙalla mutum 5 yan bindiga suka sace a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, a jihar Neja.

Idan baku manta ba, a farkon wannan shekaran wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban makarantar Islamiyya a garin Tegina.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindiga sun sake kai hari garin a ƙarshen makon nan, inda suka sace ma'aikata 5 a wata ma'aikata dake garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel