Da duminsa: Har cikin fada, 'yan bindiga sun harbe yarima, sun sace gimbiya a arewacin Najeriya

Da duminsa: Har cikin fada, 'yan bindiga sun harbe yarima, sun sace gimbiya a arewacin Najeriya

  • Tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki har cikin fadar sarki Ikpomolokpo na gundumar Gege a karamar hukumar Ado ta jihar Benue
  • Sun nemi sanin inda basaraken da matarsa suke amma Yarima Thompson ya ki sanar da su, lamarin da yasa suka harbe shi a take
  • Ba su tsaya nan ba, sun kara da dauke gimbiya inda suka nausa dajin Atiga da ita, duk da rundunar sojin yankin tana bibiyarsu

Benue - 'Yan bindiga sun kutsa fadar Ikpomolokpo na gundumar Gege da ke karamar hukumar Ado ta jihar Benue a sa'o'in farko na ranar Litinin, sun kashe yarima tare da tasa keyar gimbiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ganau ba jiyau ba sun sanar da yadda 'yan bindigan suka kutsa yankin wurin karfe 2 na dare kuma kai tsaye suka wuce fadar basaraken inda suka tada hankula.

Kara karanta wannan

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

Da duminsa: Har cikin fada, 'yan bindiga sun harbe yarima sun sace gimbiya a arewacin Najeriya
Da duminsa: Har cikin fada, 'yan bindiga sun harbe yarima sun sace gimbiya a arewacin Najeriya
Asali: Original

Mazauna kauyen sun ce sun ji harbin bindiga babu kakkautawa daga gidan basaraken amma sun kasa kai dauki saboda su kansu ba za su iya kare kansu ba, Daily Trust ta wallafa.

Shugaban karamar hukumar Ado, Chief James Oche, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Makurdi inda ya ce ya samu kiran gaggawa kan aukuwar lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wasu 'yan bindiga wurin karfe biyun dare yau Litinin sun shiga gidan sarkin Ipomoloko ta katanga kuma sun tambaya dan basaraken inda mahaifinsa da mahaifiyarsa suke.
“Matashin ya sanar da su cewa bai san inda suke ba, hakan yasa suka bindige shi inda a take ya sheka lahira kuma suka tasa keyar 'yar uwarsa," yace.

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa, da gaggawa suka sanar da rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) amma kafin su isa fadar, 'yan bindiga sun tsere zuwa dajin Atiga da ke yankin.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka fasa gilashin mota suka yi awon gaba da hamshakiyar 'yar kasuwa

Oche ya ce dakarun a halin yanzu suna bibiyar wadanda suka sace gimbiyar domin cafke su tare da ceto ta.

Har a yayin rubuta wannan rahoton, ba a samu kakakin rundunar 'yan sandan jihar ba domin ji ta bakin ta.

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun halaka rayuka 9 tare da sace shanu

A wani labari na daban, a kalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu a kauyen Tungar Ruwa da ke karamar hukumar Anka a jihar.

‘Yan bindiga sun fada wa kauyen inda suka sace dabbobi, balle shaguna sannan suka yi awon gaba da kayan abinci.

Majiyoyi sun tabbatar wa Channels Television yadda ‘yan bindigan suka fada garin da daren Laraba inda suka dinga harbe-harbe ko ta ina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel