Dalilin da yasa mutanen kirki ba su shiga siyasa a Najeriya, Gwamna Masari

Dalilin da yasa mutanen kirki ba su shiga siyasa a Najeriya, Gwamna Masari

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace dabancin siyasa ke hana mutanen kirki shiga a dama da su
  • Gwamnan ya kuma yi kira ga yan siyasa baki ɗaya su aje duk wani banbanci, su sa ilimi wajen tafiyar da harkokinsu
  • Gwamnan Yahaya na jihar Gombe, yace gwamnatinsa zata yi duk mai yuwu wa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yace rikici da kuma dabanci a siyasa ke hana mutanen kirki shiga harkokin siyasar Najeriya su bada gudummuwa.

Dailytrust tace Gwamnan Masari ya faɗi haka ne a Gombe, yayin da suka kai ziyarar a madadin kungiyar gwamnonin APC, tare da gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru.

Gwamnonin biyu sun kai wannan ziyara ne domin jajantawa gwamnatin Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, bisa rikicin siyasa da ya faru a jihar.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Gwamna Masari
Dalilin da yasa mutanen kirki ba su shiga siyasa a Najeriya, Gwamna Masari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Masari yace:

"A matsayin shugabannin siyasa, hakki ya rataya a kan mu kare rayuwa da dukiyoyin al'umma. Saboda haka a kowane irin yanayi bai kamata mu saka kanmu cikin rikicin da zai jikkata mutane ko ma ya kashe wasu ba."

Menene mafita?

Masari ya yi kira ga yan siyasa baki ɗaya da su zuba ruwan sanyi a zuƙatansu, su nuna wayewa yayin gudanar da harkokin siyasar su.

Da yake martani, Gwamna Yahaya, ya nuna matukar jin daɗinsa ga takwarorin nasa bisa nuna damuwarsu kan gwamnatin Gombe da al'ummar jihar.

Ya kuma jaddada cewa babban abinda ya rataya kan kowace irin gwamnati shine ta tsare rayuka da kuma dukiyoyin al'ummarta.

"Da zaran mun gaza kare rayuwar mutane da dukiyoyinsu, hakan na nufin mun gaza sauke hakkin dake kan mu, kuma Allah zai mana hukunci kan abinda muka yi."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya yi magana kan rahoton kisan kiyashin da akai wa masu zanga-zangar EndSARS

Matakan da gwamnatin Gombe zata ɗauka?

Gwamna Yahaya ya bayyana cewa zaman lafiyar da aka samu a jihar Gombe ya samo asali ne daga kyakkyawan shiri da kuma dabaru.

Yace gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.

A wani labarin kuma Pantami yace Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, yace nan gaba kadan za'ai mamakin matakin da Najeriya zata hau.

A cewarsa tattalin arzikin zamani na Najeriya zai shiga sahun mafi karfi a duniya nan da wasu shekaru kalilan mazu zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel