Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi magana kan rahoton kisan kiyashin da akai wa masu zanga-zangar EndSARS

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi magana kan rahoton kisan kiyashin da akai wa masu zanga-zangar EndSARS

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace gwamnatinsa ba zata zuba ido rahoton bincike kan zanga-zangar EndSARS ya wuce hakanan ba
  • Buhari yace a halin yanzun gwamnatin zata jira ta ga irin matakin da gwamnatocin jihohi zasu ɗauka, kafin ta yi martani
  • Sakataren Amurka, Antony Blinken, ya yaba da aikin da kwamitin bincike ya yi kan lamarin

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace zai jira ya ga matakan da Legas zata ɗauka, kafin gwamnatinsa ta ɗauki mataki kan rahoton binciken da aka gudanar kan zanga-zangar EndSARS.

Kwamitin da aka kafa domin bincike ya mika rahotonsa ga gwamnan jihar Legas, wanda ya kunshi cin mutuncin da yan sanda sukai wa masu zanga-zanga, da kuma buɗe wa mutane wuta a Lekki.

Kara karanta wannan

Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

The Cable tace daga cikin abinda kwamitin ya bankaɗo, yace jami'an tsaro sun hallaka "masu zanga-zangar lumana."

Shugaba Buhari
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi magana kan rahoton kisan kiyashin da akai wa masu zanga-zangar EndSARS Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Da yake jawabi yayin ganawarsa da sakataren Amurka, Antony Blinken, Buhari yace gwamnatinsa zata karbi rahoton bayan jahar Legas ta gama aiki a kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran gwamnatoci su ɗauki mataki - Buhari

Shugaban ya kuma kara da cewa sauran gwamnatocin jihohin da lamarin ya shafa, ya kamata su yi aiki kan rahoton kwamitocin su.

Buhari yace:

"Akwai gwamnatocin jihohi da dama da lamarin ya shafa, kuma sun samu rahoto daban-daban daga kwamitin binciken da suka kafa."
"Mu a matakin ƙasa, zamu jira muga matakin da jihohi zasu ɗauka kuma za mu bari su yi amfani da hangen su, ba zamu musu katsalandan ba."

Demokaradiyya ta fara aiki - Sakataren Amurka

A cewar sanarwan da mai taimaka wa shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, sakataren Amurka ya kira rahoton binciken da, 'Demokaradiyya a bakin aiki.'

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU

Ya kuma kara da cewa za su duba suga abinda ya dace a a cikin hukumomin tsaron ƙasar nan, kamar yadda Punch ta rahoto.

Me Buhari yace game da cire Najeriya daga jerin masu take yancin addini?

Kazalika da yake martani kan zare Najeriya daga jerin kasashen dake take yancin addini, Shugaba Buhari yace Najeriya zata cigaba da baiwa kowa yancin yin addininsa.

Bugu da kari, Buhari ya nuna jin daɗinsa bisa taimakon da Amurka take wa Najeriya wajen cefanar mata da makaman aiki na dakarun soji.

"Yan taimaka mana wajen dai-dauta al'amura a yankin arewa maso gabas, kuma mun samu cigaba sosai tun daga shekarar 2015."

A wani labarin kuma Hukumar Aikin Hajji ta kasa NAHCON ta tabbatar da cewa a 2022 yan Najeriya zasu samu damar yin aikin hajji

Kwamishinan labarai, tsare-tsare da bincike, Sheikh Mamoh, yace suna da tabbacin maniyya za su sauke farali a bana 2022.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro sama da 100 a jihar Benuwai

A wata fira da wakilin mu, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata su fara shiri tun yanzu domin sauke farali idan Allah ya so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel