Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami

Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami

  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, yace nan gaba kadan za'ai mamakin matakin da Najeriya zata hau
  • A cewarsa tattalin arzikin zamani na Najeriya zai shiga sahun mafi karfi a duniya nan da wasu shekaru kalilan
  • Pantami yace wannan shine buri da kudirin ma'aikatar sadarwa da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari

Bauchi - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace bada jimawa tattalin arzikin zamani zai shiga sahun mafi karfi a duniya.

The Cable ta rahoto cewa Ministan ya yi wannan furucin ne a wurin taro karo na biyu a tsangayar kimiyya da fasaha ta kwalejin fasaha dake Bauchi.

Pantami yace taken taron, 'Rawar kimiyya da fasaha da kirkire-kirekire a tattalin arzikin zamani: Domim kawo cigaba mai ɗorewa' ya na da alaƙa da manufar tattalin arzikin zamani.

Kara karanta wannan

Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro

Isa Pantami
Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami Hoto: Dr. Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Vanguard ta rahoto Ministan yace:

"Yana da matukar amfani saboda kasar mu Najeriya takai wani mataki na shiga jerin kasashen da a yan wasu shekaru masu zuwa za'ai gogayya da su ɓangaren karfin tattalin arzikin zamani."
"Wannan shine fata da burin ma'aikatar sadarwa da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma duk wata hukuma dake karkashin ma'aikatar sadarwa, masu zaman kansu, su maida hankali kan tattalin arzikin zamani."
"Kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire sune hanyoyin gano wasu ko ba duka ba hanyar kawo karshen yunwa ta hanyar zamanantar da noma, fita daga talauci, samun kyakkyawan lafiya da sauransu.

Tattalin arzikin Najeriya ya fara dai-daituwa - Pantami

Sheikh Pantami ya samu wakilcin daraktan kamfanin Galaxy Backbone Plc, Muhammad Abubakar, a wurin taron.

Bugu da kari ministan ya kara da bayyana cewa tattalin arzikin zamani na Najeriya ya fara ɗauƙan kyakkyawar hanyar haɓɓaka.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya samo mafita ga lamarin 'yan bindiga, ya bude wa Fulani makaranta

Yace hakan ya haifar da sakamako mai kyau, ta yadda kasuwanci yake bunkasa cikin tsari mai kyau, da yadda mutane ke biyan bukatunsu na bayanai da kayayyakin amfani.

A wani labarin kuma Jerin matakan da zaka bi, ka mallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

A ranar Jumu'a da ta gabata, 12 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin siyar da gidajen da ta gina ga yan Najeriya a farashi mai rahusa.

Gwamnatin ta bude sabon shafin yanar gizo domin mutane su nemi siyan ɗaya daga cikin gidajen kai tsaye daga inda suke. Mun tattara muku jerin hanyoyin da zaku bi, ku cike bayanan ku a wannan shafin domin amfana da shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel