Ko shakka sai kudin Hajji ya tashi, babu yadda muka iya - NAHCON

Ko shakka sai kudin Hajji ya tashi, babu yadda muka iya - NAHCON

  • Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa kudin aikin Hajjin bana zai tashi
  • Prince Sheikh Momoh Sulaiman ya ce ko shakka babu za a samu karin kudin Hajjin saboda yanayin tsadar abubuwa a yanzu
  • Sai dai ya bayar da tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu sauki a farashin da zaran sun dawo daga taron da za su je a kasar Saudiyya

Hukumnar kula da jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa ko shakka babu za a ga sauyi a farashin kujerar Hajjin bana.

Kwamishinan tsare-tsare, alkaluma, bincike da bayanai na hukumar aikin hajji ta kasa, Prince Sheikh Momoh Sulaiman, ya ce ba a san ransu bane za a samu kari a kudin Hajjin ba illa yanayin yadda abubuwa suke a yanzu.

Kara karanta wannan

Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyayata su shirya, NAHCON

Ko shakka sai kudin Hajji ya tashi, babu yadda muka iya - NAHCON
Ko shakka sai kudin Hajji ya tashi, babu yadda muka iya - NAHCON Hoto: Sadiq Onyesansiye Musa
Asali: Facebook

A hira da yayi da Legit Hausa, Momoh ya ce dole za a bukaci wadanda kudinsu ke kasa wanda yake tsakanin naira miliyan 1.5 da kasa da haka su yi kari a kan kudin domin samun damar sauke farali.

Ya ce sauye-sauyen abubuwa da aka samu sakamakon annobar korona da ya kaso tsaico a lamuran duniya ya shafi kasar Saudiyya ita ma wanda hakan ya sa ta kara yawan harajin da take karba daga kaso biyar cikin 100 zuwa 16%.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana farashin chanjin dala zuwa naira daga cikin abubuwan da za su sa kujerar Hajji tsada a bana.

Ya ce:

"Hajji zai kara tsada a bana babu ko shakka a kan haka. Kamar yadda yake, a wancan lokacin mutanen da suka ajiye kudin aikin hajji sun ajiye naira miliyan 1.5 ko kasa da haka, mafi yawan kudin da aka ajiye shine naira miliyan 1.5 da nufin cewa kudaden za su isa ayyukan hajji idan ba haka ba za mu mayar da wannan ba tare da rage kudaden da aka samu daga miliyan 1.5 din ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

"Amma kamar yadda yake a yanzu, komai ya karu a cikin shekarar saboda bambancin covid 19, wanda ya kawo sauyi ga rayuwa ciki harda tattalin arziki.
"Saboda haka, lamarin ya shafi kasar Saudiyya kamar yadda ya shafi kasarmu. Don haka nan take suka kara yawan kudin harajinsu wanda a yanzu suke karbar kaso 16 cikin 100 sabanin 5% na baya.
"Sannan a yanzu suka fara kara harajin biza kuma duk wadannan za su yi tasiri a kan kudin aikin hajji.
"Masauki da za ka iya samu akan riyad 2000 yanzu ya karu a kan farashin dala, wannan wata matsala ce domin a lokacin dalar Amurka ta kasance 300 da yan doriya amma kuma yanzu farashin dala ya kai N411 a dubawar karshe da nayi.
"Saboda, haka bizar da aka yi, farashinsa ya karu, dole komai zai karu a cikin kunshin aikin hajji. Don haka duk wadanda suka ajiye miliyan N1.5 sai an kirasu domin su zo su cika kudinsu.

Kara karanta wannan

'Yan ajin 'Open Diaries' sun bijirewa malama kan kudin shiga ajin WhatsApp N3k

"Karin da za su yi ya danganta da lokacin da muka dawo daga kasar saudiyya don tattaunawa da su kamar yadda suka gayyace mu wanda muke fatan zai kasance tsakanin yanzu zuwa Disamba.
"Idan muka dawo, ya kamata mu san ko nawa farashin zai kama sannan mu san abin da za mu yi game da shi.
"Har yanzu muna kokarin ganin an rage kudin hajji amma ba za mu iya rage shi fiye da abin da kudin zai iya kamawa ba. Wadanda suka cika kudin ne kawai za su iya zuwa aikin hajjin bana."

Saudi Arabiya ta kawo sababbin salo a shekarar 1443, mahajjata za su yi aikin hajji da wayoyi

Mun kuma kawo cewa akwai bambance-bambance da za a gani a aikin hajjin shekarar nan. Sheikh Momoh Sulaiman ya bayyana wannan a wata hira da Legit.ng Hausa.

Prince Sheikh Momoh Sulaiman wanda shi ne kwamishinan tsare-tsare, alkaluma, bincike da bayanai na hukumar aikin hajji ta kasa ya zanta da mu ta salula.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Kwamishinan na hukumar NAHCON ya bayyana cewa su na ta kokari domin ganin ba a bar Najeriya a baya ba a hajjin da za ayi a wannan shekara ta 1443.

Asali: Legit.ng

Online view pixel