Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyyata su shirya, NAHCON

Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyyata su shirya, NAHCON

  • Hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON ta bayyana cewa yan Najeriya za su samu damar yin aikin Hajji a 2022
  • Kwamishinan labarai, tsare-tsare da bincike, Sheikh Mamoh, yace suna da tabbacin maniyya za su sauke farali a bana
  • A wata fira da wakilin mu, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata su fara shiri tun yanzu

Abuja - Kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da kuma yaɗa labarai na hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Mamoh, yace bana yan Najeriya zasu samu damar sauke farali a kasa mai tsarki.

Prince Mamoh ya bayyyana cewa babu tantama suna da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata zasu gudanar da Hajji.

Da yake fira da Legit.ng Hausa, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata dake faɗin Najeriya su fara shiri tun yanzun.

Prince Mamoh
Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyayata su shirya, NAHCON Hoto: @Sadiq Onyesansiye Musa
Asali: Facebook

Da yake amsa tambayar da wakilin mu ya masa, yan Najeriya zasu so sani musamman maniyyata, shin akwai aikin Hajji a bana?

Kara karanta wannan

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Prince Mamoh yace:

"Eh, duk da bamu samu sako daga masarautar Saudiyya kai tsaye ba, amma zan iya cewa muna da tabbacin za'a gudanar da aikin Hajji a wannan shekaran."
"Duba da abubuwan da suka faru har suka sanya aka dakatar da Hajji sun wuce a yanzu, abinda muka sani shine aikin hajjin 2022 zai gudana Insha Allah."

Wane shiri hukumar NAHCON take yi?

Kazalika kwamishinan, wanda ke jagorantar bangaren tsare-tsare, ya kara da cewa hukumarsu na shirin kawo sauyi domin saukaka abubuwa.

A cewarsa tun bayan dakatar da aikin Hajji saboda barkewar annobar COVID19, NAHCON ta cigaba da aiki ba dare ba rana domin kara inganta aikin Hajji ta yadda yan Najeriya za su samu sauki.

Idan baku manta ba a kwanakin baya ƙasar Saudiyya, ta bada dama an gudanar da Umrah ba tare da kayyade adadi ko bin dokokin korona ba.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya samu damar zuwa gudanar da tasa Umrah, tare da yi wa Najeriya addu'ar samun zaman lafiya.

A wani labarin kuma Saudi Arabiya ta kawo sababbin salo a shekarar 1443, mahajjata za su yi aikin hajji da wayoyi

Prince Mamoh ya bayyana cewa akwai sabbin abubuwa da ƙasar Saudiyya ta kirkiro a aikin hajjin shekarar 2022 dake tafe.

Kwamishinan na hukumar NAHCON ya bayyana cewa su na ta kokari domin ganin ba a bar Najeriya a baya ba wajen aikin Hajjin na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel