Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa ƙanin Aliko Dangote rasuwa

Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa ƙanin Aliko Dangote rasuwa

  • Alhaji Sani Dangote, kanin attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya rasu
  • Marigayin ya rasu ne a kasar Amurka, a ranar Lahadi 14 ga watan Nuwamba bayan ya dade yana fama da jinya
  • Kafin rasuwarsa, Sani Dangote ne mai kamfanin Dansa kuma ya rike mukmai da dama a bangaren kasuwanci

Amurka - Sani Dangote, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma kanin Alhaji Aliko Dangote ya riga mu gidan gaskiya.

Mista Dangote ya rasu ne a kasar Amurka a ranar Lahadi 14 g watan Nuwamban 2021 bayan fama da rashin lafiya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa ƙanin Aliko Dangote rasuwa
Allah ya yi wa ƙanin Aliko Dangote rasuwa. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Duk da bai kai dan uwansa kudi ba, Sani Dangote yana da hannun jari a bangarorin noma, banki, man fetur da sauransu.

Wasu mukmai da Sani Dangote ya rike

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Har wa yau shi mamba ne na kwamitocin kamfanoni daban-daban kamar Kamfanin Simintin Dangote, Kamfanin Sukarin Dangote, Matattar Mai Da Takin Zamani na Dangote, Kamfanin Samar Da Kayan Noma na Dangote da sauransu.

Ya yi fice a lokacin da ya ke shugabancin Dansa Holdings, wani bangare na kamfanonin Dangote da ke sarrafa ababen sha kamar yadda rahoto ya nuna.

Kuma shine ya mallakin kamfanonin Dansa Foods Limited, Dansa Energy, Sagas Energy Limited, Bulk Pack Services Ltd, Dansa Agro Allied Limited da Dangote Farms Limited.

Kazalika, mamba ne a kwamitoci daban-daban na kasuwanci, kuma mamba a kungiyar masu fitar da kayyaki zuwa kasashen waje ta jiragen ruwa.

Sani Dangote ne kuma shugaban kungiyar masu hada takin zamani da samar da shi a Nigeria wato FERSAN kuma kwarren mai wasan Polo ne.

Kara karanta wannan

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa

A wani rahoton, kun ji cewa jikar tsohon Firimiyan tsohuwar Yankin Arewacin Nigeria, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ta riga mu gidan gaskiya.

Hajiya Hadiza ta rasu ne a Sokoto bayan fama da fajeruwar rashin lafiya kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

An haife ta ne a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel