Karban haraji a Sokoto: Yan bindiga sun kai hari yankin da suka ki bin umarni a Sokoto

Karban haraji a Sokoto: Yan bindiga sun kai hari yankin da suka ki bin umarni a Sokoto

  • Yan bindiga sun kai hari kauyen da suka kekashe kasa suka ki biyan miliyan N3m kuɗin haraji
  • Rahotanni sun bayyana cewa mautanen kauyen Kwarin Mai Saje, sun yi kokarin haɗa kudin amma basu iya tattara miliyan N3m ba
  • Hakan ne ya fusata yan bindigan suka farmaki kauyen, inda suka sace mutum 6 sannan suka kwashe kayan amfani

Sokoto - Miyagun yan bindiga sun kai hari kauyen Kwarin Mai Saje a karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara saboda sun ki biyan kuɗin harajin da aka ƙaƙaba musu.

Premium Times ta rahoto cewa yayin harin, yan bindigan sun ci zarafin mata kuma suka yi awon gaba da wasu mutum 6.

Mazauna garin sun tabbatar da cewa maharan sun kwashi kayayyakin amfani mallakin mutanen kauyen.

Jihar Zamfara
Karban haraji a Sokoto: Yan bindiga sun kai hari yankin da suka ki bin umarni a Sokoto Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Yankuna nawa suka sa wa haraji?

Read also

Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata

Rahoto ya nuna yan bindigan sun ƙaƙaba haraji kan kauyuka 13 a yankin, amma babu Kwarin Mai Saje a cikin waɗan da lamarin ya shafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai wata tawagar yan bindiga dake da alaƙa da sanannnen ɗan bindiga, Ada Aleru, sun saka ƙauyen Kwarin Mai Saje cikin yankunan da zasu biya su haraji.

Wani mazaunin yankin, Sama’ila Tsafe, ya bayyana cewa yan bindigan na ganin mazauna ƙauyen sun raina su, shiyasa suka ƙi biyayya ga umarnin su.

Meyasa suka ɗauki wannan matakin?

Sama'ila yace:

"Yan bindiga kusan 100 sun farmaki kauyen jiya, sun kwashe mafi yawan abubuwa masu amfani a kauyen kuma sun ci zarafin mata a gidajensu."
"Ba wai mutanen ba su son biya bane, sun gaza haɗa miliyan uku ne baki ɗaya, sun tattara dubu N600,000, amma yan bindigan suka ƙi amsa sai sun haɗa duka."

Read also

Aƙalla Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina

Ya bayyana cewa harin da aka kai wannan ƙauyen zai zama tamkar gargaɗi ga sauran kauyukan dake kokarin yin watsi da umarnin harajin.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, Muhammed Shehu, bai ɗaga kiran waya da aka masa ba kuma bai maida amsar sakonnin da aka tura masa ba.

A wani labarin kuma Shekih Ahmad Gumi yace ana masa ƙari game da matsayarsa kan ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda

Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yace ana jingina masa maganganun da bai yi ba.

Shehin malamin ya musanta maganar da ake jingina masa cewa ayyana yan bindiga a matsayin yan bindiga zai kawo karshen Najeriya.

Source: Legit.ng

Online view pixel