Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina

Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina

  • Wani sabon hari da miyagun yan bindiga suka kai jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutum 6, wasu da dama sun jikkata
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharn sun shiga ƙauyen Gwarjo, ƙaramar hukumar Matazu da daddare
  • Har zuwa yanzun rundunar yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da harin, yayin ƙauyuka ke cigaba da fuskantar matsaloli

Katsina - Hare-haren da ake kaiwa yankunan jihar Katsina na cigaba da ƙaruwa yayin da wasu mahara suka kashe mutum 6 a Gwarjo, karamar hukumar Matazu.

Premium Times ta rahoto cewa mazauna garin sun tabbatar da cewa wasu mutum 9 sun jikkata yayin harin na ranar Jumu'a da daddare.

Wani mazaunin ƙauyen, Musa Abdullahi, yace yan bindiga sun shiga garin da misalin ƙarfe 9:00 na dare, suka cigaba da mummunan nufinsu har tsawon awa 4 kafin su fice da kusan 1:00 na dare.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da jana'iza a Benuwai

Harin Katsina
Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mutumin yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun shigo da misalin karfe 9:00 na dare, suna isowa suka bude wuta kan mai uwa da wabi. Mutum shida suka mutu yayin haka, wasu 9 suka jikkata."

Ya mutanen gari suka yi?

Abdullahi ya bayyana cewa waɗan da suka samu raunuka an kai su asibitin Amadi Rimi Orthopaedic da kuma babban asibitin cikin Katsina.

Ya bayyana sunayen waɗan da suka mutu da Abdu Bahillace, Ali Niga, Bello Yusuf, Dan Asabe Ubi, Sanin Ayya da kuma Abdullahi Bello.

Shin maharan sun sace wasu?

Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro, yace akwai mutane da dama da suka ɓata, amma ba maharan ne suka sace su ba.

Yace:

"Wasu daga cikin yan uwanmu, sun dawo gidajen mu da zama, kuma mun ji labarin cewa wasu da dama sun tsorata kuma suka tsere cikin jeji domin tsira da rayuwarsu."

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan Katsina, Gambo Isa, ta wayar salula, bai ɗaga kiran ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

A wani labarin kuma Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP da yawa a wani kwantan bauna a jahar Borno

Dakarun sojin Operation Hadin Kai (OPHK) na bataliyar ta 82 sun yi wa mayakan ISWAP/Boko Haram mummunan ɓarna a yankun Pulka, jihar Borno.

Sojojin sun samu wannan nasara ne tare da taimakon jami'an sakai na JTF, da yan bijilanti bayan samun bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel