Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun sake kai harin Tegina, sun yi awon gaba da ma'aikatan ruwa

Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun sake kai harin Tegina, sun yi awon gaba da ma'aikatan ruwa

  • Yan bindiga sun sake kai hari garin Tegina dake jihar Neja, bayan harin da suka kai Isamiyya a farkon shekarar nan
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun shiga wata ma'aikatar ruwan Leda, inda suka yi awon gaba da akalla mutun 5
  • Har zuwa yanzun hukumar yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da lamarin, wanda ya faru a karshen makon nan

Niger - Dailytrust ta ruwaito cewa aƙalla mutum 5 yan bindiga suka sace a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, a jihar Neja.

Idan baku manta ba, a farkon wannan shekaran wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban makarantar Islamiyya a garin Tegina.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindiga sun sake kai hari garin a ƙarshen makon nan, inda suka sace ma'aikata 5 a wata ma'aikata dake garin.

Kara karanta wannan

Aƙalla Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun sake kai harin Tegina, sun yi awon gaba da ma'aikatan ruwa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Rahoto ya bayyana cewa maharan da suka sake kai hari garin sun kai aƙalla 10, kuma ɗauke da bindigun AK-47.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta shaida mana cewa yan bindigan sun mamaye kauyen ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Asabar kuma suka nufi ma'aikatar ruwan leda 'Pure Water.'

Majiyar tace:

"Maharan sun shammace mu domin a kafa suka zo, kawai mun fara jin ƙarar harbin bindiga bayan sun bude wuta, nan fa muka fara tseren tsira da rayuwar mu."
"Daga nan sai suka nufi kamfanin ruwan leda 'Pure Water' inda suka tattara mutum 5 suka yi awon gaba da su."

Wane mataki jami'an yan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace yana cikin taro ne a lokacin da aka neme shi.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun halaka rayuka 9 tare da sace shanu

Amma ya ɗauki alkawarin yin magana bayan ya kammala taron, amma har zuwa lokacin haɗa rahoton nan bai ce komai ba.

A wani labarin kuma Gwarazan yan sanda sun fatattaki tsagerun yan bindiga, sun ceto mutane da dabbobi a jihar Katsina

Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta dakile harin wasu tsagerun yan bindiga a Gidan Duka, karamar hukumar Kankara.

Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah, shine ya sanar da haka, yace an kuma kwato shanu da tumaki da dama a hannun su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel