Bance ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda zai kawo karshen Najeriya ba, Sheikh Ahmad Gumi

Bance ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda zai kawo karshen Najeriya ba, Sheikh Ahmad Gumi

  • Shekih Ahmad Gumi yace ana masa ƙari game da matsayarsa kan ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda
  • A cewarsa sama da kashi 99 cikin ɗari na makiyaya ba su da hannu a ayyukan yan bindiga
  • Ya shawarci gwamnatin tarayya ta gina wa yan bindigan nan makarantu domin a shirye suke su aje makamansu

Kaduna - Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yace ana jingina masa maganganun da bai yi ba.

Tribune Online ta rahoto Shehin malamin ya musanta maganar da ake jingina masa cewa ayyana yan bindiga a matsayin yan bindiga zai kawo karshen Najeriya.

Malamin ya bayyana cewa sam bai faɗi haka ba, mutane ne ba su fahimnci abinda yake nufi ba.

Shiekh Ahmad Gumi
Bance ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda zai kawo karshen Najeriya ba, Sheikh Ahmad Gumi Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Gumi ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai yayin ziyarar gani da ido a cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio a Kauyen Kahoto, wanda gidauniyar Sultan Bello ta gina wa makiyaya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata

Ko me Gumi yake nufi da maganarsa?

Sheikh Gumi yace kashi 99% na fulani makiyaya ba su da hannu a ayyukan yan bindiga, kuma idan aka ayyana makiyaya a matsayin yan ta'adda za'a samu matsala.

Vangaurd ta rahoto Sheikh Gumi yace:

"Kashi 99 cikin dari na mutanen nan ba su da hannu a aikata ayyukan yan bindiga, idan aka ayyana su a matsayin yan ta'adda, Najeriya zata shiga matsala ta ko ina."
"Me kuma ya yi saura idan aka cewa kowane ɓangaren Najeriya yana ci da wuta? Idan aka sake makiyaya suka shiga rikicin addini, kasar nan zata shiga tasku."

Menene mafita?

Shehin malamin ya shawarci gwamnatin tarayya, maimakon kokarin kashe biliyoyin kudi wajen siyo makamai, kamata yayi ta gina makarantu.

Ya kara da cewa ya zanta da tawagar yan bindiga da dama kuma sun tabbatar masa da cewa a shirye suke su aje makamansu su rungumi ilimi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da jana'iza a Benuwai

Da yake magana kan makarantar, Gumi yace cibiyar tana kunshe a azuzuwan karatu 6, wanda za'a cigaba da bada karatu awa 24 a kullum.

"Makiyaya zasu fita kiwon dabbobinsu da safe, idan kuma sun dawo da yamma su halarci wurin ɗaukar karatu."
"A halin yanzu zamu fara karatun Firamare da Sakandire. Muna da Asibiti a cibiyar, kuma za'a koya musu yadda zasu kara zamanantar da kiwon dabbobinsu."

A wani labarin kuma Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023

Sheikh Sani Yahaya Jingir yace babu wanda ya isa ya siyar da kuri'un mutane da sunan karba-karba a 2023.

Shehin Malamin ya kira tsarin da wani abu mai kama da caca, kuma a cewarsa mutane kada su yarda da shi kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel