Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

  • Masu kallo su na tsaka da shaukin kallon shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in, kwatsam aka wayi gari daya daga cikin jaruman shirin fim din ta yi aure
  • Da safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamban 2021 aka wayi gari da batun auren Rahama MK, matar gwamna Bawa Mai Kada da ke cikin shirin
  • Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, an yi shagalin bikin ne a gidan su da ke birnin Kano a sirrance don ba a bayyana wa mutane da dama ba

Kano - Ana tsaka da more shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in sai aka wayi gari da batun auren sirri da wata jarumar fim din ta yi.

Jaridar Dimokardiyya ta ruwaito cewa, Rahama MK, wacce ta fito a matsayin matar Gwamna Bawa Mai Kada ta yi auren ta a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zamu Janye Malamai Daga Yankunan Da Ba Tsaro, an Halaka Guda 800, Ƙungiyar Malamai Ta Ƙasa

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri
Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri. Hoto daga dimokaradiyya.com.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.

Tuntuni an samu labari a kan batun auren jarumar amma ba ta fadi lokaci da kuma wanda za ta aura ba, hakan ya sa mutane su ka dinga mamaki.

Yayin da wakilin jaridar Dimokuradiyya ya bukaci jin ta bakin jarumar ta bayyana cewa:

“Dama na shaida cewa zan yi aure tun kwana 3 da su ka gabata, kuma ga shi Allah ya tabbatar kuma ya cika min buri na.”

Ta kara da addu’ar Allah ya ba ta haihuwa kuma ta yi fatan mutuwa a dakin mijin ta.

Batun fina-finai kuma ta ce za ta ci gaba da fitowa a shirin Kwana Casa’in, amma sauran babu tabbas.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

A wani labari na daban, shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Booth, ta sa an cafke mata wani matashi da ta zarga da yada labarai na karya kan ta inda aka sa shi yin bidiyo domin neman afuwar ta da janye miyagun kalamansa.

A kwanakin baya, labarin cewa Maryam Booth ta koka da yadda ba a saka ta fina-finai tun bayan bayyana bidiyon tsiraicin ta ya bazu.

Kamar yadda kagaggen labarin ya bayyana, jarumar ta shiga damuwa kuma ta ce ta na neman miji ido rufe domin ta yi aure ta huta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel