Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

  • A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da suka sa har yanzu ba ta dage dakatarwar da aka yiwa shafin Twitter ba
  • Ministan yada labarai, Mohammed ya bayyana cewa ba a dage dakatarwar bane saboda har yanzu kamfanin bai biya bukatun da FG ta bayar ba
  • Ministan ya bayyana cewa Najeriya bata haramta Twitter ba, ta dakatar da shi ne kawai kuma dakatarwar ba ta da alaka da batutuwan da suka shafi shugaba Muhammadu Buhari

Paris - Rahoton da jaridar The Nation ta fitar na nuni da cewa gwamnatin tarayya ta ce ba a dage dakatarwar da aka yi wa shafin Twitter ba saboda kamfanin ya cika sharudda 10 ne kacal daga cikin 12 da aka gindaya masa.

Read also

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

Sai dai gwamnatin ta kara da yi wa ‘yan Najeriya fatan cewa lokaci ya yi da za a shawo kan duk wata matsala ta Twitter.

Yanzu-Yanzu: Buhari bai hakura ba, ba a dage dokar hana Twitter ba a Najeriya
Minstan yada labarai, Lai Mohammed | Hoto: vanguardngr.com
Source: Depositphotos

Hakazalika, ta bayyana cewa dakatar da shafin Twitter ba shi da alaka da batutuwan da suka shafi shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayar wata da ta halarci taron ta jefa masa a wurin taron hadin gwiwa na Najeriya na International Partnership Forum a birnin Paris.

Yawancin masu saka hannun jari a dandalin sun nuna sha'awar sanin halin da ake ciki bayan dakatar da Twitter.

Mohammed, wanda ya yi magana da harshen Faransanci cikin kwarewa, ya kama hankalin masu sauraro ba tare da sun san ya kware a yaren ba.

Read also

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

Wacce ta jefa tambayar a taron, ta rude kuma ta yi mamakin ganin kwarewar Ministan a yaren Faransanci.

Amma Mohammed ya dauki lokaci wajen bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba a dage dakatarwar da aka yiwa Twitter ba.

Yace:

“Ina son in fadi cewa Najeriya ba ta haramta Twitter ba, an dakatar da shi ne kawai, don haka ba a haramta Twitter ba, an dakatar da shi ne.
“Hakazalika, dakatarwar ba ta da alaka da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Maganganun da ke tsakaninmu da Twitter sun kai wani mataki babba. Ina so in bayyana cewa maganar da ake yi da musayar da ake yi sun yi tasiri sosai.
"Amma muna da wasu 'yan batutuwa da za mu warware. A cikin kusan sharudda 12, Twitter ya sami damar cika 10.
"Ba da jimawa ba, za a warware dukkan batutuwan ta yadda zai yi kyau ga kasarmu da kuma Twitter."

Read also

Sai anyi tsarin yaki da rashawa na gaba-gadi kafin Najeriya ta tsira, Sanata Ndume

Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar dakatarwa a Najeriya

A wani labarin, Gwamnatin tarayya, ta hanyar ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ta sanar da dage dokar hana Twitter, kana kamfanin zai bude ofishinsa a Najeriya.

Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, yayin da yake zantawa da wakilan gidan gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.

Ministan ya ce ya zuwa yanzu, gwamnati ta dage dakatar da shafin tare da wasu sharudda wadanda wasu daga ciki sun hada da yin rijista da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC).

Source: Legit.ng

Online view pixel