Sokoto: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar malamin addini, sun bakaci Naira miliyan 30 kudin fansa

Sokoto: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar malamin addini, sun bakaci Naira miliyan 30 kudin fansa

  • Wasu masu garkuwa da mutane sun sace matar Rabaran Oro Yakubu, sakataren cocin ECWA na jihar Sokoto
  • Yan bindigan sun sace matar malamin addinin ne a hanyar Lambar Bakura zuwa Lambar Tureta yayin zuwa Sokoto daga Tsafe
  • Sun kuma nemi a biya Naira miliyan 30 kudin fansa amma daga bisani suka sako zuwa Naira milyan 2.5 amma sun saka wa'adi

Jihar Sokoto - 'Yan fashin daji sun yi garkuwa da matar sakataren cocin Evangelical ta Afirka ta yamma, ECWA, reshen jihar Sokoto, Rabaran Oro Yakubu.

Jaridar SaharaReporters ta ruwaito cewa masu garkuwan sun bukaci a biya su Naira miliyan 30 kudin fansa kafin su sako ta.

Sokoto: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar malamin addini, sun bakaci Naira miliyan 30 kudin fansa
'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar malamin addini a Sokoto, sun bakaci Naira miliyan 30 kudin fansa. Hoto: Vanguard NGR
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace mutum 5, sun sanya sabon haraji kan garuruwan Sokoto

An rahoto cewa an sace ta ne a hanyar Lambar Bakura zuwa Lambar Tureta yayin zuwa Sokoto daga Tsafe.

SaharaReporters ta gano cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalanta, sun bukaci a biya su Naira Miliyan 30 daga bisani aka yi ciniki ya koma Naira miliyan 2.5.

Masu garkuwar sun saka wa'adin biyan kudin

Yan bindigan, daga nan sun bada wa'adi zuwa karfe 7 na safen ranar Juma'a a biya kudin fansar.

Sun yi barazanar cewa idan lokacin ya yi ba a biya kudin ba hakan zai tilasta musu daukan matakin da ba zai yi dadi ba.

Cocin na ECWA yana baran addu'o'i a yayin da ya ke kokarin hada kudin.

Wani mamban cocin ya ce:

"Don Allah ku yi wa Rabaran Yakubu Oro da dukkan cocin ECWA ta Sokoto addu'a."

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel