‘Yan bindiga sun sace mutum 5, sun sanya sabon haraji kan garuruwan Sokoto

‘Yan bindiga sun sace mutum 5, sun sanya sabon haraji kan garuruwan Sokoto

  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane biyar a wani hari da suka kai garin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto
  • A wannan karon sun bukaci al'umman yankin da su biya N500,000 a matsayin kudin fansar mutanen
  • Hakan na zuwa ne kimanin wata guda bayan maharan sun karbi naira miliyan 11 a matsayin kudin fansa domin sakin mutane 20 da suka yi garkuwa da su a garuruwan yankin

Sokoto - Kimanin wata guda bayan karbar naira miliyan 11 a matsayin kudin fansa domin sakin mutane 20 da suka yi garkuwa da su a garin Gatawa, 'yan bindiga sun sake dawowa garin a ranar Laraba.

A wannan karon, maharan sun sake sace mutane biyar, inda suka nemi a biya N500,000 a matsayin kudin fansarsu, kamar yadda majiyoyi suka bayyana a garin.

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

‘Yan bindiga sun sace mutum 5, sun sanya sabon haraji kan garuruwan Sokoto
‘Yan bindiga sun sace mutum 5, sun sanya sabon haraji kan garuruwan Sokoto Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A baya garin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto na daya daga cikin garuruwan da basu san hare-haren 'yan bindiga ba.

Amma kuma a yanzu tsagerun sun mayar da hankali wajen kaddamar da hare-harensu a garin, rahoton Premium Times.

A harin na ranar Laraba, wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa saboda tsaro, ya fada ma jaridar cewa 'yan bindigar basu kashe kowa ba amma dai kawai sun mayar da hankali ne wajen ganin an tara masu kudade.

Majiyar ta ce:

"Sun zo ne da misalin karfe 8:00 na safe lokacin da yawancin mutane ke fitowa daga gidajensu. Sun yi harbi da dama a sama kafin suka fara garkuwa da mutane. Da suka tara wasu adadi na mutane, sai suka yanke shawarar kyale mata su tafi amma suka yi awon gaba da mazaje biyar. Bayan sun tafi, sai suka aiko da wani sako cewa mu tara masu N500,000 a matsayin kudin fansa."

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

Ya ce Gatawa na cikin garuruwan da 'yan bindiga suka nemi su tara naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar wadanda aka sace daga garuruwan a watan da ya gabata. Ya ce garin Gatawa ta tara naira miliyan 1 a waccan lokacin.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wani lakcara kuma dan jarida, Mansur Isa, ya tabbatar da lamarin.

Isa ya ce:

"'Yan bindigar sun umurci mutanen Gatawa da su kawo kudin fansar tsakanin yau Alhamis da Litinin. An sanya ma kowani gida harajin N2,500 amma ba lallai ne kudin ya isa ba don haka yanzu muna tuntubar yan garin da ke zaune a wasu wuraren domin a samu a hada kudaden a kan lokaci."

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun kuma umurci wani gari a yankin, Tarah, da su biya naira miliyan 7 a matsayin nasu harajin.

Usman Tarah, wani mazaunin garin, ya ce 'yan bindigar sun aika wani sako a ranar Talata kuma mutane sun fara harhada kudi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

Tarah ya ce:

"'Yan bindigar da muke tunanin masu biyayya ga Bello Turji ne sun bukaci da mu biya naira miliyan bakwai. Watsi da tabarbarewar tsaro a wasu yankunan Sokoto da gwamnati tayi yana baiwa 'yan bindiga damar cin karensu ba babbaka tare da kwasar mutane aiki cikin sauki. Abun da muke fuskanta a yanzu somin tabi ne."

Mohammed Shehu, wani mazaunin Tarah, ya ce sun yi mamaki lokacin da suka samu sako daga 'yan bindigar suna umurtansu da su hada fansar, saboda ba a sace ko mutum guda daga mutanensu ba.

"Ba mu san dalilin da yasa suka nemi mu biya miliyan bakwai ba kuma suma basu fadi komai ba kan dalilin da yasa aka ci tararmu ba. Amma ka san ba za mu iya yi masu tambayoyi ba."

Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar bai dauki wayansa ba ko amsa sakon tes da ke neman jin ta bakinsa kan wannan rahoto ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

'Yan sanda sun karyata jita-jitan cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a Sokoto

A baya mun kawo cewa rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta ce 'yan bindiga ba su nada sabbin hakimai da cin tarar mazauna garin Sabon Birni ba.

A kwanan nan 'yan bindiga suka kai munanan hare-hare a karamar hukumar Sabon Birni.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin 'yan sandan jihar, Sanusi Abubakar, ya ce bincike ya nuna cewa babu kamshin gaskiya a ikirarin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel