Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

  • Yan bindiga sun kai farmaki yankin Anara, a karamar hukumar Isiala Mbano da ke jihar Imo inda suka ta harbi ba kakkautawa
  • Lamarin wanda ya afku a daren Talata, 9 ga watan Nuwamba, ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane biyar
  • Zuwa yanzu ba a ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar kan lamarin ba domin yana cikin wani taro

Isiala Mbano, Jihar Imo - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane biyar a yankin Anara, karamar hukumar Isiala Mbano da ke jihar Imo.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun far ma garin ne a daren ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba.

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi
Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi Hoto: The Nation
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin da aka ambata da suna Damian ya bayyana cewa mutane da dama basu ritsa ba a garin sakamakon karar harbe-harbe da maharan suka dunga yi a iska.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta saurayi da budurwa da aka kama suna jima'i a kan titi da rana tsaka a bainar jama'a

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hankalinmu ya kasance a tashe a gaba daya daren yayin da karar harbi ya karade yankinmu. A yanzu haka da nake magana, ko kaza ba za a gani a waje ba."

Wani mazaunin yankin ya ce a ranar Laraba, wasu mutane sun karade garin, inda suka bukaci mutane da su bi umurnin zaman gida na kungiyar awaren IPOB.

Kungiyar IPOB dai ta umurci al'umman yankin kudu maso gabas da su zauna a gida a duk lokacin da za a gurfanar da shugabanta, Nnamdi Kanu a gaban kotu.

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa kan sabon lamarin, kakakin yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam, ya bukaci wakilin Daily Trust ya sake kiransa domin yana a cikin wata ganawa.

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani kyaftin din soji mai ritaya

A wani labari na daban, yan bindiga a yammacin ranar Juma'a, sun bude wa wasu fasinjoji wuta a mahadar Umulogho a karamar hukumar Obowo ta jihar Imo inda suka kashe uku nan take, rahoton The Nation.

Harbin, da aka yi misalin karfe 7.50 na yamma, ya janyo tashin hankali a yayin da mazauna gari da masu wucewa suka cika wandunansu da iska don tsira.

A cewar wasu da abin ya faru a idonsu, sun ce maharan nan take suka tsere a cikin motarsu suka nufi Umuahia a jihar Abia yayin da suka bar mutane ukun a kwance cikin jini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel