'Yan sanda sun karyata jita-jitan cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a Sokoto

'Yan sanda sun karyata jita-jitan cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a Sokoto

  • 'Yan sanda a jihar Sokoto sun karyata rade-radin cewa yan bindiga sun nada sabbin hakimai a kauyukan Sabon Birni
  • Kakakin rundunar, Sanusi Abubakar, ya ce bincike ya nuna cewa ikirarin ba komai bane face kanzon kurege
  • Ya kuma bayyana cewa rundunonin tsaro sun kaddamar da ayyuka na musamman a yankunan da ke fama da ta'addanci a jihar domin dawo da zaman lafiya

Sabon Birni, Jihar Sokoto - Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta ce 'yan bindiga ba su nada sabbin hakimai da cin tarar mazauna garin Sabon Birni ba.

A kwanan nan 'yan bindiga suka kai munanan hare-hare a karamar hukumar Sabon Birni.

'Yan sanda sun karyata jita-jitan cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a Sokoto
'Yan sanda sun karyata jita-jitan cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a Sokoto Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin 'yan sandan jihar, Sanusi Abubakar, ya ce bincike ya nuna cewa babu kamshin gaskiya a ikirarin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

A cewar Abubakar, rundunar 'yan sandar ta dauki matakai da dabaru da dama domin tantance gaskiyar ikirarin.

Ya ce rundunonin tsaro na aiwatar da ayyuka domin dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ta'addanci ya shafa a jihar, ruwayar Daily Trust.

Sanarwar ta ce:

"An ja hankalin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto kan wannan labarin da ke yawo a yanar gizo da sauran kafofin watsa labarai cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a kauyukan Sabon Birni da kuma tursasa biyan tara.
"Rundunar na amfani da wannan damar domin sake jadadda wa jama'a musamman mazauna jihar Sokoto cewa, rundunar bata yi kasa a gwiwa ba a yaki da take yi da yan fashi da sauran masu aikata laifuka a jihar.
"Bincike ya nuna cewa ikirarin cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a kauyukan Sabon Birni ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

"Mun kuma yi amfani da dabaru da dama da kuma jami’an leken asiri don tantance tushen wannan ikirarin.
"Sai dai kuma, akwai wani aiki da ke gudana a karkashin “Operation Hadarin Daji” da suka hada da sojoji, yan sanda, rundunar sojin sama da kuma tawagar tsaro na musamman. Nan ba da dadewa ba, za a kai wannan aiki zuwa sansanin ‘yan fashi, kuma za a dawo da zaman lafiya a yankunan da ayyukan ‘yan fashin suka shafa.”

Kakakin yan sandan ya bukaci yan jarida da jama'a da su ci gaba da ba jami'an tsaro goyon baya a yaki da suke da fashi da makami da sauran ayyukan ta'addanci a jihar.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A baya mun ji cewa yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Gwamnati ta karyata rahoton cewa mutane na tururuwan barin Anambra

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel