Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

  • 'Yan bindiga sun farmaki Gidan-Kwano, gefen jami'ar fasaha ta tarayya (FUT) da ke garin Minna a jihar Neja
  • A yayin harin, 'yan bindigar sun yi garkuwa da mutane biyu sannan suka kashe wani mazaunin yankin daya
  • Kakakin yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin inda ya ce sun yi nasarar daidaita lamarin tare da kama mutum daya

Minna, jihar Neja - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai wani hari yankin Gidan-Kwano, gefen jami'ar fasaha ta tarayya (FUT) da ke garin Minna, babbar birnin jihar Neja.

Maharan sun halaka mutum daya sannan sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a harin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna
Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kai tsaye maharan suka kaddamar da ta'asarsu a gefen babban mashigin jami'ar kuma an tattaro cewa daliban da ke zama a wajen makarantar sun fi yawa ne a garin da lamarin ya afku.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Majiyoyi sun sanar da jaridar cewa 'yan bindigar sun kai farmakin ne a safiyar ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin amma ya ce an daidaita lamarin.

Sai dai kuma, bai ce komai ba a kan mutuwar wani mazaunin yankin.

Ya ce:

"Da misalin karfe 23:30, wasu da ake zaton yan baranda ne sun kai farmaki wani shago a Gidan-Kwano gefen babbar mashigin FUT Minna sannan suka sace yaran mai shagon su biyu.
"Yan sanda da yan banga sun yi gaggawar zuwa wajen domin farautar yan daban kuma a yayin bincike, an kama daya daga cikin wadanda ake zargi a kauyen Barkuta."

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

A wani labari makamancin haka, mun kawo cewa akalla mutane 15 ciki harda matan aure uku ne suka rasa ransu a kauyukan Binnari da Jab Jab a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Binnari da misalin karfe 4:00 na asuba a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, inda suka dunga harbi kan mai uwa da wabi.

An tattaro cewa mutanen kauyukan sun yi yunkurin yakar su amma sai yan bindigar wadanda yawansu ya fi 50 suka sha karfinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel