Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

  • Mataimakin kakakin majalisa a jihar Borno ya bayyana yadda 'yan ta'addan ISWAP suka barnata gidan Dan uwansa
  • Ya ce, sun kai hari yankinsu, inda suka kone godan yayansa tare da barnata wurare da yawa a cikin garin a yayin harin
  • An ruwaito cewa, mazauna garin sun tsere daga cikin garin da kewayensa domin tsira da rayukansu daga 'yan ta'addan

Borno - Abdullahi Musa Askira, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, ya bayyana yadda wasu da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne suka kona gidan yayansa a wani hari da suka kai kwanan nan.

A zantawarsa da Daily Trust, dan majalisar ya ce gidan da ke unguwar Chan Chan Dana da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar, an lalata shi ne a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa
Konannen gida | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yadbayyana cewa:

“A jiya ne wasu ‘yan ta'adda suka kai hari garinmu, inda suka kona gidan yayana marigayi wanda shi ne hakimin kauyen kafin ya mutu kusan shekara guda da ta wuce.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ni ne na gina masa shi; amma ba gidana bane... Kafin su zo su kai hari kauyenmu da safiyar ranar, sojoji sun je matsuguninsu suka tarwatsa su. Don haka, abin takaici har yanzu da saura. Duk da haka, za mu ci gaba da tallafa wa sojojinmu da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a yankinmu."

Legit.ng Hausa ta tattaro muku a baya cewa, an ruwaito mazauna garin sun tsere daga cikin garin da kewayensa lokacin da ‘yan ta’addan suka far wa garin a ranar Laraba.

Akwai damuwa game da karuwar rashin tsaro a fadin kasar nan, musamman a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata an kashe mutane 31 a hare-haren da aka kai a jihohin Taraba, Katsina da Imo.

A ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka bindige ‘yan sanda bakwai a wani harin kwantan bauna da suka kai a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindiga sun shiga gidajen mutane sun tafka barna

A wani labarin, ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Asali: Legit.ng

Online view pixel