Jiragen saman NAF sun fara aikin rakiya ga jiragen kasa masu jigilar Abuja zuwa Kaduna

Jiragen saman NAF sun fara aikin rakiya ga jiragen kasa masu jigilar Abuja zuwa Kaduna

  • Hukumomin sojoji sun fara kokarin kare ‘yan Najeriya masu tafiye-tafiye ta hanyar jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja
  • An girke wasu sojojin saman Najeriya a wannan hanya domin tabbatar da lafiyar fasinjojin da ke cikin hanyar ta jirgin kasa
  • Wani harin baya-bayan nan da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai kan jirgin ka iya zama dalilin da yasa sojojin suka fara sintiri daga sama

Rundunar sojin Najeriya ta aike da wasu jirage masu saukar ungulu don sanya ido kan hanyar jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja.

Mukaddashin daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Birgediya-Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Da dumi-dumi: An girke sojoji domin sintiri a hanyoyin jirgin kasa
Matakin kan harin jiragen kasa | Hoto: Jerrywright Ukwu
Asali: Original

Legit.ng ta tattaro cewa, duk da cewa Birgediya-Janar Onyeuko bai ce komai ba kan sabon shirin, amma ya tabbatar da cewa an fara aikin sintirin.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

Da aka nemi karin bayani kan atisayen na soja, Onyeuko ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

''Muhimmin abu shi ne kasancewar rundunar sojojin saman Najeriya a layin dogon. Ya isa a ce an fara aikin. Ko da ta tafiya kuke a kan tituna, za ku ga jirage masu saukar ungulunmu a kan wannan hanya.’’

An sha kai hare-hare a kan jiragen kasa da layin dogo daga wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba.

Hare-hare biyu na baya-bayan nan sun faru ne a daren ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba da kuma safiyar ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.

A yayin da ya ke martani kan lamarin, wani tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani, ya ce ‘yan bindigar sun dasa wasu abubuwan fashewa a hanyar jirgin kasan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

A cewar Shehu Sani, bama-baman da ‘yan bindigar suka dasa sun lalata wani bangare na layin dogon wanda ya hana zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar jirgin Kaduna zuwa Abuja.

Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya da shugabannin hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya da su dauki mataki kan ‘yan bindiga.

Bayan shawarar tsohon dan majalisar, NRC ta dakatar da duk wani motsi na jiragen kasa na tsawon kwanaki biyu don baiwa gwamnati damar magance matsalolin tsaro.

Jami’an hukumar ta NRC sun ce an kuma dakatar da ayyukan layin dogon yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ko da gaske ne an jefa bam a cibiyar kamar yadda ake hasashe.

A wani mataki na gaggawa, manajan daraktan hukumar ta NRC, Fidet Okhiria, ya ce 'yan fasa kwabri ne suka kai hari kan jirgin.

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

A wani labarin, ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel