Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

  • Rahoto ya bayyana cewa, wasu miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun fatattaki wani kauye a jihar Borno
  • A halin da ake ciki, sun fatattaki kowa a garin, lamarin da jawo asarar dukiyoyi da kone gidaje masu yawa
  • An ce sojoji sun fita da sarkin garin, duk da haka mutane sun fara dawowa bayan lafawar harin na Boko Haram

Borno - Mazauna garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno sun tsere lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari wani kauye ranar Laraba.

Daily Trust ta ce ta samu labari daga majiyoyi cewa ‘yan ta'addan da suka kai harin da safe sun kona gidaje da dama.

Wani ganau ya ce maharan sun kai farmaki a yankin Krangla, mai tazarar kilomita takwas da garin.

Da dumi-dumi: Boko Haram sun kai hari kan mazauna a Borno, sun kone gidaje
'Yan ta'addan Boko Harm | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Getty Images

Yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa cikin daji da kuma tsaunuka da ke kewaye domin tsira da rayukansu, rahotanni sun ce jerin gwanon sojoji sun yi wa basaraken yankin rakiya daga wajen garin.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki Askira Uba, mutane sun gudu daga muhallansu

Bulama Jonah, daya daga cikin iyayen ‘yan matan Chibok da aka sace, ya ce ya tsere daji da wasu mutane da dama inda suka boye har lamarin ya dan lafa.

Ya ce:

"Mun garzaya daji domin tsira; kowa yana gudu ne kawai saboda mun ji sun kona Krangla kuma suna tafiya zuwa Askira."
“Mun dawo garin, duk da cikin tsoro, bayan mun ji sojoji sun shiga domin su tare su kafin su isa nan. Har yanzu sojoji suna nan.”

Wani direba dan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da jim maharan na kan hanyarsu, sai ya gudu da matarsa mai ciki.

A ranar Litinin din da ta gabata The Cable ta ruwaito yadda 'yan Boko Haram suka yi musayar wuta da sojojin Najeriya duk dai a jihar ta Borno.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

A wani labarin, ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel