Hayaniya ta barke a majalisar dattijai kan shirin saka wasu jihohi uku a jerin masu fitar da man fetur

Hayaniya ta barke a majalisar dattijai kan shirin saka wasu jihohi uku a jerin masu fitar da man fetur

  • Wata yar hayaniya ta barke a majalisar dattawan Najeriya yayin da aka gabatar da kudirin garambawul a hukumar NDDC
  • Sanata Adeola daga jihar Legas, ya gabatar da kudirin ne wanda ya kunshi saka jihohi uku cikin masu samar da albarkatun man fetur
  • Sai dai lamarin baiwa sanatocin da suka fito daga Neja Delta dadi ba, inda suka yi fatali da kudirin

Abuja - Sanatocin da suka fito daga Niger Delta sun yi fatali da kudirin takwarorin su na saka Bauchi, Legas da Ogun a jerin masu samar da ɗanyen mai.

Dailytrust tace mahawara ta barke a majalisar ne yayin da aka fara nazari kan kudirin garambawul na dokar da ta samar da hukumar raya Neja Delta NDDC.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Garambawul ɗin zai kunshi saka waɗan nan jihohi uku da kuma wasu da suka fara samar da albarkatun man fetur a Najeriya.

Majalisar dattawa
Hayaniya ta barke a majalisar dattijai kan shirin saka wasu jihohi uku a jerin masu fitar da man fetur Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jihohi 9 dake cikin hukumar NDDC sun haɗa da, Cross River, Edo, Delta, Abia, Imo, Bayelsa, Rivers, Akwa-Ibom da Ondo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya tada hayaniyar tun farko?

A zaman majalisar, kudirin ya samu tsallake karatu na biyu, wanda sanata Solomon Olamilekan Adeola (APC, Lagos) ya gabatar da shi.

Adeola yace tuni jihohin Bauchi, Legos da Ogun suka shiga jerin masu samar da ɗanyen man fetur, bayan gano albarkatun mai a Alkaleri, Badagry da Ipokia.

The Cable ta rahoto Sanatan yace:

"Bisa adalci, jihohin sun cancanci samun kashi 13 da ake ware wa jihohin dake samar da ɗanyen mai kamar yadda sashi na 162 sakin baka na 2 na kundin mulki ya tanadar."

Kara karanta wannan

Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin daura Aure

"Mai girma shugaban majalisa, na gabatar da wannan kuduri ne domin waɗan nan jihohi su shiga jerin masu albarkatun mai da ma wasu da za'a iya samu nan gaba."

Kudirin bai wa wasu daɗi ba

A nasu martanin, sanatoci daga yankin Neja Delta, sun yi watsi da kudirin na kokarin saka jihohin Bauchi, Legas da Ogu cikin NDDC.

Sanatocin George Sekibo (PDP, Rivers), Matthew Urhoghide (PDP, Edo) da Ovie Omo-Agege (APC, Delta), sun ce an kirkiri NDDC ne domin magance gurbatar muhalli a yankin.

Urhoghide yace jihohin dake wajen Neja Delta na da damar samun tagomashin kashi 13 da ake ware wa, amma ya jaddada cewa saka su a NDDC ya saba wa doka.

Sanatocin sun roki Adeola ya canza tunani, ya nemi a samar da hukumar da zata duba yanayin a yankin kudu maso yamma, maimakon neman saka Legas da wasu a cikin NDDC.

Me sanatocin Arewa suka faɗa?

Kara karanta wannan

Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi a Gombe

A nasu ɓangaren sanatocin da suka fito daga Arewa, sun nuna goyon bayansu ga kudirin amma sun nuna cewa jihohin dake wajen yankin Neja Delta bai kamata su shiga NDDC ba.

A wani labarin kuma Hukumar ICPC ta bankado yadda aka karkatar da ayyukan mazabu sama da 300 a Jigawa da Kano

Hukumar ICPC ta bayyana cewa ta gano yadda aka aiwatar da ayyukan mazabu 300 a jihohin Jigawa da Kano.

A cewar shugaban ICPC mai kula da jihohin, Garba Kagara, hukumarsa ta umarci yan kwangila da yan majalisu su koma su gyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel