Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi

Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi

  • Sanata Danjuma Goje ya nemi IGP da Malami su gudanar da bincike kan harin da aka kai masa a ranar Juma'a lokacin da yaje jihar Gombe
  • Lauyan tsohon gwamnan na Gombe ya bayyana cewa harin wani yunkuri ne na kashe Goje da mukarraban Gwamna Inuwa Yahaya suka yi
  • A ranar Juma'a da ta gabata ne dai wasu da ake zaton yan daba ne suka hana Goje shiga garin Gombe

Jihar Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje ya nemi Sufeto Janar na 'yan sanda, Alkali Baba da babban Atoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami da su binciki harin da aka kai masa.

Goje ya yi zargin cewa harin da aka kai masa a Gombe yunkuri ne na hallaka shi da hadiminsa, Adamu Manga.

Read also

Kwana guda bayan harin da aka kai wa mahaifinta, 'Yar Goje ta ajiye aikin Kwamishina a Jihar Gombe

Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi
Rikcin Goje da Inuwa: Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Ya yi zargin cewa dogarin gwamna Inuwa Yahaya, Zulaidaini Abba da shugaban tsaron gwamnan, Sani Bajoga sune manyan wadanda ake zargi, rahoton Punch.

Lauyan Goje, VC Nwadike ne ya rubuta wasikar mai kwanan wata 8 ga watan Nuwamba, an kuma karbe shi a ofishoshin IGP, AGF da Darakta Janar na DSS a ranar Litinin.

Sanatan ya bukaci IGP ya binciki lamarin da nufin hukunta jami'an da ke da hannu a lamarin bayan an dauki matakin ladabtarwa a kan su, rahoton Premium Times.

Wasikar ta rubuto lambar aiki ADC din a matsayin AP/No:118814 da na babban shugaban tsaron a matsayin AP/No :57675.

Wani bangare na takardar na cewa:

"Cewa a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2021, wanda muke karewa ya shigo Gombe ta filin jirgin sama na Gombe da misalin 10:30 don halartan daurin auren dan uwansa sannan wasu magoya bayansa na mazabunsa suka zo don tarbansa a filin jirgin tare da yi masa rakiya zuwa gida.

Read also

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

"A hanyarsu ta zuwa gidan wanda muke karewa, sai SP Zulaidaini Abba da Sani Bajoga, babban mai tsaron gwamnan jihar suka far ma hadiminsa da sauransu da bindigogi, adduna da sauran makamai.
"Ikon Allah ne kadai ya tsiratar da wanda muke karewa, amma hadiminsa ya taki rashin sa'a domin maharan sun ji masa mummunan rauni.
"A wani waje kusa da cibiyar taro na filin jirgin saman Gombe, babban titin Bauchi-Gombe, ADC da CSO sun jagoranci Kawu Keep, maharan Sanusi, Danjuma Skade da sauransu, sun zo da motoci da dama mallakar gidan gwamnati da yan daba da dama a bayansu."

'Yan daba sun hana Sanata Goje shiga garin Gombe, sun tare hanya suna ƙone-ƙone

A baya mun kawo cewa wasu da ake zargin yan daba ne, a ranar Juma'a, sun hana Sanata Muhammad Goje shiga garin Gombe.

Goje, wanda ya tafi Gombe domin halartar daurin aure, ya dira a filin saukan jirage na Gombe a Lawanti misalin ƙarfe 10.40 na safe.

Read also

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda ake zargi yan daban ne sun tare babban titin Gombe-Bauchi kusa da International Conference Centre, sun cinna wuta a titi sun hana shiga ko fita daga Gombe.

Source: Legit.ng

Online view pixel