Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin bikin Aure

Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin bikin Aure

  • Wasu miyagun yan bindiga sun yi yunkurin garkuwa da ɗan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom a wurin bikin aure
  • Honorabul Usoro Akpanusoh, ya bayyana cewa maharan shi suka so sace wa amma ya samu nasarar tserewa, amma sun kashe mutum 2
  • Kwamishinan yan sandan jihar ya umarci jami'ai su gudanar da bincike kan lamarin tare da kame maharan

Akwa Ibom - Wasu tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum biyu yayin da suka yi kokarin garkuwa da ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Usoro Akpanusoh, a wurin bikin aure.

PM News tace shirin garkuwa da ɗan majalisan, inda bai samu nasara ba ya auku ne a ƙauyen Uquo, karamar hukumar Esit Eket, ranar Alhamis da ta gabata.

Sai dai lamarin bai fito ba sai yau Talata yayin da ɗan majalisa, Akpanusoh mai wakiltar Esit Eket/Ibeno, a majalisar dokokin jihar, ya bayyana wa manema labarai.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin gini mai hawa 21 da yan uwansa kan gadon kudaɗe da motocin alfarma

Akpanusoh
Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin bikin Aure Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ta ya Dan majalisan ya tsira?

Yace maharan sun farmaki wurin taron bikin auren da nufin su sace shi, amma sai Allah ya ɗora shi a kansu har ya samu nasarar tsira daga sharrin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ɗan majalisan ya kuma miƙa godiyarsa ga Allah bisa ba shi nasara har ya kuɓuta daga yunkurin garkuwa da shi bayan ya koma gidansa dake kauyen Uquo.

Yace:

"Naje wurin bikin aure a Uquo na iyalan mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a gunduma ta.Na shafe mintuna 40 a wurin, sannan na yi wa ma'auratan bankwana."
"Lokacin da na yi nufin shiga motata, kwatsam sai ga wata mota Nissan Sony ta iso, ba da jimawa ba wani ya fito da bindiga AK-47 ya fara harbi a sama."
"Naga sanda ya fara saita bindigan zuwa Motata, daga nan sai ya fara harbin mutane, nan take ya bindige mutum 2."

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Kan Hanya: Barayin da suka sace masu ibada 60 a Kaduna sun bukaci buhunan shinkafa da jarkokin mai

Yadda maharan suka so sace ɗan majalisan

Akpanusoh ya ƙara da cewa maharan sun yi yunkurin sace shi, bayan sun fitar da direbansa daga motar.

"Cikin sa'a direban ya cacimi ɗaya da faɗa har ya samu nasarar sake shiga cikin mota ya tuƙa mu"

Ya kuma tabbatar da cewa sauran mutanen da suka jikkata daga harbin bindigan maharan an gaggauta kai su asibiti, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sandan jihar, SP Odiko Macdon, yace tuni kwamishinan yan sanda ya bada umarnin gudanar da bincike.

"Muna da masaniyar an yi yunkurin sace ɗan majalisar dokoki, a halin yanzun hukumar yan sanda na kokarin gano maharan."

A wani labarin kuma wani Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi babban kamu a majalisar dokoki, inda wani ɗan majalisa ya sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da mata zalla a Neja

Kakakin majaisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya sanar da sauya shekar Ajao Adejumo, daga ADP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel