Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikata na kananan hukumomi 13

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikata na kananan hukumomi 13

  • Dalibai karkashin gammayar kungiyoyin arewa, CNG, sun yi barazanar dakatar da harkoki a Zaria
  • Daliban sun yi barazanar daukan wannan matakin ne biyo bayan sace ma'aikatan kananan hukumomi 13 da yan bindiga suka yi
  • Yan bindigan sun tare ma'aikatan ne a yayin da suke dawowa daga ta'aziyya suka tisa keyarsu cikin daji

Zaria, Kaduna - Bangaren dalibai na gammayar kungiyoyin arewa, CNG, ta yi barazanar dakatar da harkoki cak a Zaria, jihar Kaduna bisa sace ma'aikatan kananan hukumomi 13 a jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda abin ya faru da su suna dawowa ne daga wurin ta'aziyya.

Wasu daga cikin wadanda aka sace sun hada da Direktan Ilimi da Cigaban Al'umma, Mrs Deborah Mugu da mataimakinta, Dalhatu Aliyu Awai.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatana kananan hukumomi 13
Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatana kananan hukumomi 13. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun ce an sace su ne a Kidandan a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranar Litinin.

Wata majiyar tsaro ta ce an sako Umar Abubakar (Katako), direban motar mai daukan mutum 18 da ya dakko ma'aiakatan.

An ruwaito cewa an sake shi ne domin ya tafi ya shaidawa iyalan ma'aikatan cewa an sace yan uwansu.

Yadda lamarin ya faru

Ya ce, bisa bayanai da ganau suka bayar, yan bindigan kimanin su shida dauke da AK-47 ne suka tare motar kimanin mintuna 45 bayan sun baro garin Kaya.

Ya kara da cewa bayan yan bindigan sun kammala bincikar fasinjojin da kwace musu kayayyaki, sun umurce su da su shiga cikin daji.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel