Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya

Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya

  • Bayan da gwamnatin Buhari ta sanar da dakatar da dokar hana Twitter, kamfanin ya magantu kan lamarin
  • Ya tabbatar da hakan ta bakin wani kakakinsa, kamar yadda aka ruwaito daga tushe mai kyau
  • Hakazalika, gwamnati ta bayyana wasu ka'idoji da kamfanin da Twitter zai cika kafin kafa ofishi a Najeriya

Abuja - Gwamnatin tarayya, ta hanyar ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ta sanar da dage dokar hana Twitter, kana kamfanin zai bude ofishinsa a Najeriya.

Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, yayin da yake zantawa da wakilan gidan gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.

Ministan ya ce ya zuwa yanzu, gwamnati ta dage dakatar da shafin tare da wasu sharudda wadanda wasu daga ciki sun hada da yin rijista da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC).

Jaridar Punch ta bayyana cewa wasu sharuddan sune tilastawa Twitter daukar wakili dan kasa, yin rajista tare da kungiyoyi kamar NIPDA, kamar NCC, NBC, da jajircewar yin aiki tare da Ma'aikatar Haraji ta Tarayya don biyan haraji.

Kara karanta wannan

FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya

A cewar Mohammed, Twitter ya mayar da martani game da yanayin tabbatar da zama a Najeriya ta hanyar bude ofishi a 2022.

Bayan Buhari ya amince ya yafe wa Twitter, kamfanin ya yi martan
Shafin Twitter | Hoto: reuters.com
Asali: UGC

Kamfanin Twitter ya mayar da martani kan shirin gwamnatin tarayya na dage dakatarwar da aka yi kan ayyukan dandalin na sada zumunta a Najeriya.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa za a dage dakatar da ayyukan na Twitter “cikin 'yan kwanaki.”

Twitter ta yi martani

Biyo bayan kalaman ministan, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun Twitter yana cewa kwanan nan kamfanin ya gana da gwamnatin tarayya kan yadda za a warware batutuwan da suka haifar da dakatarwar.

Kakakin wanda ba a bayyana sunansa ba ya ce:

"Manufar mu ita ce mu tsara hanyar ci gaba don dawo da Twitter ga kowa a Najeriya.
"Muna fatan ci gaba da tattaunawa tare da gwamnatin Najeriya tare don ganin an maido da aikin ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito bayanin kakakin na Twitter wanda ta ambaci AFP a matsayin tushenta labarinta.

FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya

A wani labarin daban, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa nan babu dadewa gwamnatin tarayya zata dage dokar haramta Twitter da tayi a Najeriya.

Mohammed ya sanar da hakan ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa da suka yi ta yanar gizo wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A yayin bada bayanin sasancin gwamnati da Twitter, kamar yadda The Nation ta ruwaito, minsitan yace tuni Twitter ta amince da kusan dukkan sharuddan da Najeriya ta saka mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel