Sai anyi tsarin yaki da rashawa na gaba-gadi kafin Najeriya ta tsira, Sanata Ndume

Sai anyi tsarin yaki da rashawa na gaba-gadi kafin Najeriya ta tsira, Sanata Ndume

  • Sanata Ali Ndume ya nuna damuwarsa kan hanyoyin da gwamnati ke bi wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya
  • Ya bayyana bukatar fara yaki da cin hanci da rashawa ta bin tsarin gaba-gadi, inda ya kamata a fara daga sama zuwa kasa
  • Ya Kuma bayyana cewa, ya kamata shugaba Buhari ya rattaba hannu kan bukatar ayyana dukiyar da ba a san asalinta ba

Ibadan, Oyo - Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya yi Allah-wadai da matakin da ake bi na yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a yanzu, yana mai cewe daga sama zuwa kasa ya kamata a fara.

Ya kuma jaddada cewa ya kamata a fara yaki da cin hanci da rashawa tun daga kan ’yan siyasa, manyan ma’aikatan gwamnati har zuwa ma’aikatan kananan hukumomi idan har ana so a iya dakile wannan matsala, Leadership ta ruwaito.

Read also

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Sai anyi tsarin yaki da rashawa na gaba-gadi kafin a ci gaba a Najeriya, Sanata Ndume
Sanata Ali Ndume | Hoto: channelstv.com
Source: Facebook

ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da lacca mai taken: “Dukiya da ba a bayyana ba da kuma yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya”, a jerin laccoci na musamman na jami’ar Ibadan na shekarar 2021.

Ndume ya lura cewa cin hanci da rashawa na yin tasiri ga tattalin arzikin jama’a kuma yana kokarin fadada gibin da ke tsakanin wadanda suke da shi da wadanda ba su da shi.

Ndume ya jaddada cewa kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu ya samo asali ne daga cin hanci da rashawa, inji rahoton Vanguard.

Ya kuma kara da cewa cin hanci da rashawa da rashin tsaro suna da alaka da kudaden gudanar da laifuffukan da ke tsakanin ƙasashen duniya kamar ta'addanci, fataucin mutane, harkallar muggan kwayoyi da cinikin makamai ba bisa ka'ida ba.

Read also

Gwamnan Neja ya gano hanyar dakile 'yan bindiga, za a kakabawa makiyaya haraji

Ya yi kira ga Buhari da ya gaggauta rattaba hannu a kan kudirin ayyana kadarorin da ba a ayyana ba tare da mikawa Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da dokar da ta shafi laifuffuka cikin lokaci, ba tare da la’akari da cece-kuce kan yadda ake tafiyar da kudaden da aka kwato ba.

Tun da farko, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Kayode Adebowale, ya bayyana cewa, cibiyar tana yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar da ta dace, inda ya kara da cewa kusan duk dalibin da ya kammala karatun digiri a jami’ar yana daukar kwas a fannin da’a.

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, ya ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama mai matukar wahala.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wani taro tare da shugabannin kudu maso gabas a Owerri yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar Imo.

Read also

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya nakalto shugaban kasar a cikin wata sanarwa a shafin Facebook yana mai cewa babu wanda zai tuhume shi da mallakar kamfanoni ko manyan gidaje a ko ina cikin kasar nan.

Source: Legit.ng

Online view pixel