Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

  • Babban Darakta Janar na NYSC ya ziyarci jihar Anambra a kokarinsa na aikin sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a zaben gwamnan jihar da ke guda a jiya Asabar
  • Shugaban ya gana da 'yan bautan kasa a rumfunan zabe daban-daban na jihar don gane wa kansa yadda abubuwa ke tafiya daga gudunmawar 'yan bautan kasa
  • Ya jinjina musu bayan jin yadda ayyukan ke tafiya daidai, inda ya bukace su day kasance masu kara jajircewa da bin ka'idoji da dookin da aka gindaya

Anambra - Premium Times ta rahoto cewa, Babban Darakta Janar na kungiyar yi wa kasa hidima (NYSC), Shua’ibu Ibrahim, ya yabawa kishin kasa da ‘yan kungiyar da ke gudanar da aikin zaben gwamna a jihar Anambra.

Mista Ibrahim ya yi wannan yabon ne a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da yake sa ido kan zaben a kananan hukumomi tara na jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

Yabon ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC Adenike Adeyemi ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa
Darakta Janar na NYSC | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Punch ta ruwaito Daraktan yana bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mambobin kungiyar sun rubuta sunayensu a kudin tarihii, bayan da suka bayar da gudunmawa wajen tabbatar da sahihin tsarin zabe."

Ya kuma umarce su da su kasance masu nuna kishin kasa da kuma gudanar da ayyukansu bisa ka’idojin da aka kafa.

A duk rumfunan zabe da ya ziyarta, ‘yan NYSC sun sanar da shi cewa an gudanar da zaben cikin lumana.

Shirin wayar da kai

A batu makamancin haka, shugaban ya ziyarci sansanin NYSC na dindindin a jihar Anambra.

A can ne ya wayar da kan su kan tsare-tsare guda hudu na shirin, sannan ya bukace su da su rika bin dokokin NYSC da ka’idoji a wuraren aikinsu da aka turasu.

Kara karanta wannan

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

Malam Ibrahim ya bukaci ’yan bautar kasa n da su zama abin koyi mai kyau ga na baya a karshen hidimarsu.

Masu kada kuri'a sun fusata

A wani labarin daban, Fusatattun masu kada kuri'a sun garkame wasu daga cikin jami'an hukumar zaben mai zamanta kanta (INEC) ranar Asabar a Anambra.

Daily Trust tace lamarin ya faru a College Primary School, dake gundumar Oko II, karamar hukumar Orumba ta arewa. A cewar daya daga cikin sa ido a zaben, rikiciya fara ne daga lokacin da ma'aikatan suka yi kokarin komawa cibiyar karban sakamakon karamar hukuma, su bar gunduman baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel