Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

  • 'Yan sanda a jihar Yobe sun kame wasu Fulani da suka yiwa junansu rauni ta hanyar datse hannayen junansu
  • A halin yanzu ba sa cikin hayyacinsu, kuma an kwantar dasu a asibiti domin duba lafiyar su da kuma bincike
  • Rundunar 'yan sanda ta ba da umarnin bincike kan masu yawo da muggan makamai da ka iya tada hankalin jama'a

Yobe - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Yobe sun kama wasu matasan Fulani guda biyu da suka datse hannayen juna a wani fada a kauyen Bakin-Ruwa da ke Garin-Alkali a karamar hukumar Bursari a jihar.

Rahotanni sun ce an kama Fulanin biyu suna fada da juna da adduna da sanduna wanda daga baya ya yi muni har da zubar jini, SaharaReporters ta ruwaito.

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna
Taswirar jihar Yobe | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mutanen biyu sun datse hannayen juna daga wuyan hannun hagu na kowanne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce mutanen su ne; Adamu Bukar Moh’d mai shekaru 25 da Bukar Audu mai shekaru 25, an kama su ne bayan da bayanai suka isa ofishin ‘yan sanda na Garin-Alkali da sanyin safiyar ranar.

Ya ce:

"Har yanzu ba a bayyana dalilin fadan ba saboda dukkan wadanda ake zargin ba sa cikin hayyacinsu kuma an kwantar da su a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Nguru domin duba lafiyarsu."

A cewar Abdulkarim, rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kuma bukaci jami’an ‘yan sanda reshen jihar da su dauki kwakkwaran matakai na hana matasa yawo da muggan makamai kamar su wukake, adduna da sauran su abubuwan da za a iya amfani da su wajen tayar da hankula.

Kara karanta wannan

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

Iko sai Allah: Bidiyon matasan fasinjoji 2 suna ba hammata iska a cikin jirgin sama

A wani labarin, Wani bidiyon maza biyu fasinjoji a cikin jirgin suna bai wa hammata iska a cikin jirgi ya karade kafafen sada zumunta.

Babu shakka mazan majiya karfi sun fusata da juna tunda bidiyo ya nuna yadda ake ta yin kokarin raba su amma abun ya ci tura.

Kamar yadda aka gano, sun kwashi damben ne sakamakon hatsaniyar da suka samu tare da rashin jituwa wurin ajiye kayansu a cikin jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel