An kuma: 'Yan bindiga sun sace wani attajirin Zamfara a karo na biyu bayan ya tsere daga hannunsu

An kuma: 'Yan bindiga sun sace wani attajirin Zamfara a karo na biyu bayan ya tsere daga hannunsu

  • Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani attajirin dan kasuwa, Aminu Jangeme a jihar Zamfara
  • Wannan shine karo na biyu da 'yan bindigar ke yin garkuwa da Jangeme, domin a shekarar da ta gabata ma sun sace shi amma Allah ya kubutar da shi kafin a kai ga biyan fansa
  • An tattaro cewa tun bayan da ya tsere suke ta nemansa domin ya kwashe iyalinsa sun bar gari

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga a jihar Zamfara, sun sake garkuwa da wani attajirin dan kasuwa, Aminu Jangeme, shekara daya bayan ya tsere daga hannunsu.

An yi garkuwa da dan kasuwar wanda aka fi sani da Sarki a kauyensa tare da wasu mutane shida a shekarar 2020.

An kuma: 'Yan bindiga sun sace wani attajirin Zamfara a karo na biyu bayan ya tsere daga hannunsu
An kuma: 'Yan bindiga sun sace wani attajirin Zamfara a karo na biyu bayan ya tsere daga hannunsu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yayin da ake tattauna batun biyan kudin fansarsa, sai Allah ya bashi sa'ar tserewa sannan ya gudu garin Gusau tare da iyalinsa, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Jaridar Daily Post ta kuma rahoto cewa Jangeme ya dawo kauyen ba tare da ya san cewa 'yan bindigar na nan suna nemansa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa sun sake yin garkuwa da shi a gonarsa da ke hanyar Gusau-Dansadau a ranar Alhamis da ta gabata.

Yayansa, Mallam Adili, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya nuna tsoron cewa watakila maharan ba za su sake shi ba a wannan karon saboda sun dade suna nemansa tun bayan da ya tsere.

Ya kuma ce:

"Maharan sun yi ta kokarin sake yin garkuwa da shi tun a lokacin da ya tsere sannan a yanzu da suka yi nasarar damke shi, babu wanda zai iya fadin yaushe za su sake shi."

Zamfara: ‘Yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar ceto mutane 2 daga hannun ‘yan bindiga bayan kwashe makwanni 2 a hannun su.

A wata takarda da Mohammed Shehu, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya gabatar wa Premium Times ya ce sun gudanar da bincike ne sannan su ka gano inda su ke.

Bisa ruwayar Premium Times, an sace su ne a Kaura Namoda sannan an ceto su a dajin Dumburun da Gidan Jaja da ke karamar hukumar Zurmi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel