Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu

Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Rijiya da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara inda suka halaka mutum shida
  • Bayan isar su, sun dinga harbe-harbe inda suka halaka jama'a tare da shiga gidaje suna bincike tare da sace mutane
  • Kamar yadda mazaunin yankin ya sanar, miyagun sun shiga gida-gida inda suka dinga karbar kayan abinci da na amfaninsu

Zamfara - Miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka shida tare da sace wasu masu yawa a farmakin da suka kai kauyen Rijiya da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin kauyen, Mustapha Ibrahim, ya sanar da Premium Times a waya cewa 'yan bindigan sun tsinkayi yankin a tsakar ranar Lahadi.

"Sun fara harbi daga shigarsu kauyen. Ina tunanin domin su ruda mutane ne suke hakan. Sun halaka mutum shida yayin harbi. Mun kirga gawawwaki shida cif," yace.

Kara karanta wannan

Matsolo ne, baya bani kuɗi: An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta

Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu
Zamfara: 'Yan bindiga sun shiga gidaje suna karbar abinci, sun sheke mutum 6 tare da sace wasu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda yace, 'yan bindigan sun dinga shiga gida-gida inda suka dinga karbar kayan abinci da abubuwan bukatarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta ruwaito cewa, ya kara da cewa, sun bincike gida-gida kuma sun sace mutane masu yawa a hakan.

"Ba mu san yawan wadanda suka sace ba har yanzu saboda wasu sun tsere zuwa cikin daji kuma ba su dawo ba har dare. A yanzu safiyar Litinin, ba mu fara kirga ba amma sun kwashe mutane da yawa, ballantana mata da kananan yara," Ibrahim yace.

Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe Rufai, Sani Lawal da Murtala. Ya ce za a birne mamatan kuma sauran da suka samu rauni suna asibiti.

Hanyar da 'yan bindiga suka biyo

Ibrahim ya kara da cewa, 'yan bindigan da suka kai musu farmaki sun shiga yankinsu ne ta wurin Tsafe.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe Limamin Masallacin Juma'a da yaki yarda a tafi da shi, sun sace yaransa

Tsafe ta na da iyaka da Gusau, babban birnin jihar. Yankunan Gusau ballantana masu kusanci da Tsafe suna fama da matsalar farmakin miyagun.

'Yan bindiga sun harbe mutum 7 har lahira a kauyen Adamawa

A wani labari na daban, a kalla rayuka bakwai ne wasu miyagun 'yan bindiga suka harbe a gundumar Bolki ta karamar hukumar Numan a jihar Adamawa.

Miyagun dauke da makamai sun kai farmaki yankin Negga ne wurin karfe 11 na daren Talata kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, farmakin da miyagun suka kwashe sama da sa'a daya suna kaiwa ya bar mutane masu tarin yawa da miyagun raunika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel