Zamfara: ‘Yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su

Zamfara: ‘Yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su

  • ‘Yan sandan jihar Zamfara sun samu nasarar ceto mutane 2, bayan makonni 2 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya bayyana
  • A cewarsa rundunar ta samu nasarar ne bayan gudanar da bincike inda aka nemo su bayan sace su da a ka yi a Kaura Namoda an gano su a dajin Dumburun da Gidan Jaja da ke karamar hukumar Zurmi
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba N. Elkanah ya jajanta wa wadanda lamarin ya faru da su akan wahalhalu da azabar da su ka fuskanta a lokacin da su ke hannun ‘yan bindigan

Jihar Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar ceto mutane 2 daga hannun ‘yan bindiga bayan kwashe makwanni 2 a hannun su.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun gano mabuyar ‘Yan bindiga a kauyukan Kaduna, sun buda masu wuta

A wata takarda da Mohammed Shehu, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya gabatar wa Premium Times ya ce sun gudanar da bincike ne sannan su ka gano inda su ke.

Zamfara: ‘Yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su
'Yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su a Zamfara: Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bisa ruwayar Premium Times, an sace su ne a Kaura Namoda sannan an ceto su a dajin Dumburun da Gidan Jaja da ke karamar hukumar Zurmi.

Kakakin ya bayyana yadda aka mika su asibiti don duba laifiyar su bayan nan su ka tattauna da ‘yan sanda.

Kamar yadda takardar ta zo:

“Kwamishinan ‘yan sanda, Ayuba N. Elkanah ya jajanta wa wadanda aka ceto sakamakon wahalhalun da su ka sha lokacin su na hannun ‘yan bindigan.
“Ya tabbatar wa jama’an jihar cewa da taimakon ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su tabbatar sun yi aiki tukuru don kawo garanbawul akan matsalar garkuwa da ke faruwa a jihar.

Kara karanta wannan

Bamu yarda da su ba: Amotekun ta kama wasu ƴan arewa 18 cikin trelar wake a Ogun, ta ce su koma inda suka fito

“Kwamishinan ya yi kira ga jama’a akan su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai don ganin bayan duk wasu ‘yan ta’adda da ke jihar.”

Duk da dokokin tsaro, ‘yan bindiga sun ci gaba da aika-aika

Jihohi kamar Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi da ke yankin arewa maso yamma da jihar Neja ta arewa ta tsakiya, suna fama da rashin tsaro mai tsanani kusan shekaru 10 kenan.

Bayan dokokin tsaro da gwamnonin jihohi su ka dauka, har yanzu ‘yan bindiga su na ci gaba da kai wa mutane farmaki ta hanyar garkuwa da jama’a.

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel