Gwamnatin Neja ta rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Minna

Gwamnatin Neja ta rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Minna

  • Gwamnatin jihar Neja ta rusa wani gida mai dakuna hudu mallakar wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a Minna
  • Kwamishinan kananan hukumomi, harkokin sarauta da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, ya tabbatar da hakan yayin da yake sanya ido lokacin da ake rusa ginin
  • Umar ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta yarda kasarta ta zama mafakar masu aikata laifi ba

Minna, Jihar Neja - Wani rahoton TVC News ta kawo cewa gwamnatin jihar Neja ta rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane.

Kwamishinan kananan hukumomi, harkokin sarauta da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, wanda ya sanya ido a kan rushe gidan, ya ce wanda ake zargin ya fallasa cewa ya gina gidan ne da kudaden da ya samu daga ta'asar.

Read also

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

Gwamnatin Neja ta rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Minna
Gwamnatin Neja ta rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a Minna Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Gidan, wanda ya kasance mai dauke da dakuna biyu da wani bangare da ba a kammala ba yana a yankin Nkangbe da ke karamar hukumar Bosso a jihar.

Umar ya ce an dauki wannan matakin ne domin ya zama gargadi ga sauran miyagu cewa gwamnatin jihar ba za ta yarda masu laifi su mayar da jihar mafakarsu ba, rahoton Daily Trust.

Sai dai kuma, kwamishinan ya ki bayar da cikakken bayani kan ko wanene mai garkuwa da mutanen da kuma yadda aka gano gidansa.

Umar ya ce:

"Wannan ginin mallakar wani mai garkuwa da mutane da aka kama ne.
"Ribar laifin ne kuma tsarinmu ne rashin bari kowani laifi ya samu duwawun zama a wannan jihar.
"Za mu iya kafa wannan kuma daga yanzu, ba za mu bari wani mai laifi ya samu gurbi a kasarmu ba.

Read also

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

"Yana daga cikin kudurin gwamnan na tabbatar da ganin jihar Neja ta kasance da cikakken tsaro a gare mu baki daya."

Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi sannan su bayar da bayanai game da bakin mutane da ke ya da zango a garuruwansu.

“Mun gana da masu ruwa da tsaki a jihar Neja, kungiyoyin masu gidajen haya, masu wuraren shakatawa da kowa da kowa kuma mun fada musu cewa su kai rahoton duk wani motsi ko wani bako da ya shigo garin.
"Ina fatan za mu sami karin bayani don yin aiki da kuma tabbatar da tsaron jihar."

Gwamnan Neja ya gano hanyar dakile 'yan bindiga, za a kakabawa makiyaya haraji

A wani labarin, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa za a dawo da tsarin karbar harajin shanu da aka fi sani da “Dogali” a jihar domin yaki da ‘yan bindiga da satar shanu a jihar, Leadership ta ruwaito.

Read also

Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin

Gwamnan jihar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna ranar Alhamis 4 ga watan Nuwamba.

Ya ce matakin zai kuma baiwa gwamnati damar samun bayanan da ake bukata kan adadin shanu da kuma zirga-zirgarsu a cikin jihar.

Source: Legit.ng

Online view pixel