An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

  • Wasu bata gari da ake zargin yan 'yan bindiga ne sun kai hari a Yagbak da Ungwan Ruhugi a karamar hukumar Zangon Kataf
  • Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a inda ya ce an halaka mutane, an kona gidaje
  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi Allah wadai da harin ya kuma bukaci hukumar bada agaji na SEMA ta kai wa wadanda abin ya shafa dauki

Kaduna - An kai wa wasu garuruwa biyu hari a jihar Kaduna, inda aka yi wa wasu mutane rauni sannan aka kone gidaje a cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar.

Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, NewsWireNGR ta fitar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama
An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Ya ce:

"Sojoji da yan sanda sun sanar da gwamatin jihar Kaduna kan hare-haren da aka kai a Yagbak da Ungwan Ruhugi a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
"A cewar rahotannin, an kashe wasu mutane sannan an yi wa wasu rauni, yayin da aka kona wasu gidaje da dukkan garuruwan biyu."

Gwamnatin na jihar Kaduna ta yi kira mutanen jihar su kwantar da hankulansu a yayin da ake jiran cikaken rahoto daga rundunar sojoji, yan sanda da DSS.

Za cigaba da sanarwa mutanen gari abin da ke faruwa da zarar an tabbatar a cewarsa.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi Allah wadai da harin sannan ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, sannan ya umurci hukumar jihar na bada taimakon gaggawa, SEMA, ta yi nazarin asarar da aka yi ta tallafawa mutanen.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel