Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin

Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin

  • A kalla an samu gawawwakin mutum 20 a cikin kwana biyu da rushewar gini mai hawa 21 a Ikoyin Legas
  • Sai dai jama'a na ganin cewa ceton da ake yi yana tafiyar hawainiya saboda a kalla sama da mutum 50 ke cikin ginin
  • Hatta mamallakin ginin, an gano ya na ciki duk da da an fito da gawar mataimakiyarsa ta musamman a ranar Talata

Ikoyi, Legas - Yawan mutanen da suka rasa ransu bayan faduwar bene mai hawa 21 da ke yankin Ikoyi a jihar Legas ya kai 20 a ranar Talata duk da ana cigaba da ceto wadanda ginin ya danne.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an samu wannan karin ne yayin da aka tashi da shi mai hawa biyu a Legas a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin
Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Masana sun koka da yadda kokarin ceto jama'an ke tafiyar hawainiya tun bayan aukuwar lamarin a ranar Litinin, kusan sa'o'i talatin da shida bayan ibtila'in.

Sama da mutum hamsin ne aka gano sun makale a rusasshen ginin yayin da aka fito da kusan mutum 5 a ranar da lamarin ya faru.

Har yanzu ana cigaba da cece-kuce kan aukuwar lamarin ko bayan da gwamnatin jihar Legas ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano abinda ya janyo ibtila'in.

Dakatar da babban manajan cibiyar kula da gine-ginen jihar Legas, Gbolahan Oki, bai hana jama'a bayyana fusatarsu ba inda suka ce wannan ya nuna cin amana ce karara wacce aka bai wa hukumar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar binciken gaggawan ta hada da hukumar NEMA, LASEMA da ta kwana-kwana wadanda suka bayyana a wurin tun bayan rushewar ginin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani gini mai hawa-hawa ya sake ruftawa a jihar Legas

Masana sun ce ya dace a ce sun samu wata nasara ta ceto jama'a idan da sun mayar da hankali.

Asalin mamallakin ginin, Femi Osibona, an gano ya na cikin ginin amma har yanzu babu amon shi balle labarin shi duk da an fito da gawar wata budurwa wacce aka gano cewa mataimakiyarsa ce ta musamman.

Hukuma: Hawa 15 muka amince ya gina, amma ya wuce makadi da rawa

A wani labari na daban, babban manajan hukumar kula da gine-ginen jihar Legas ta LASBCA, Gbolahan Oki ya bayyana gaskiyar lamari dangane da ruftawar bene mai hawa 21 na jihar Legas.

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ce hukumar su ta amince da gina hawa 15 ne, amma mai benen ya toshe kunnuwan sa ya gina hawa 21.

A wata hira da wakilin NAN ya yi da Oki ta wayar salula, ya shaida masa cewa yanzu haka mai benen ya na hannun hukuma, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Yadda manyan gine-gine 8 suka ruguje a Najeriya cikin shekaru 15

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel