Yan bindiga sun kai farmaki, sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a kudadancin Kaduna

Yan bindiga sun kai farmaki, sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a kudadancin Kaduna

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki kauyukan Yagbak da Ungwan Ruhugo da ke karamar hukumar Zango-Kataf na jihar Kaduna
  • An tattaro cewa maharan sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a harin na ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba
  • Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da ya fitar

Zangon Kataf, Jihar Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kauyuka biyu na Yagbak da Ungwan Ruhugo a masarautar Ayap da ke karamar hukumar Zango-Kataf na jihar Kaduna a ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba.

An tattaro cewa akalla mutane 10 ne suka rasa ransu a harin da aka kai daya daga cikin kauyukan.

Yan bindiga sun kai farmaki, sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a kudadancin Kaduna
Yan bindiga sun kai farmaki, sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a kudadancin Kaduna Hoto: Punch
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan.

Kara karanta wannan

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

Sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumomin soji da na yan sanda sun sanar da gwamnatin jihar batun hare-haren da aka kai a wuraren guda biyu, jaridar The Guardian ta kuma ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce gwamnan ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da a je ta duba wajen sannan ta bayar da kayan rage radadi ga garuruwan da lamarin ya shafa.

A sanarwar mai taken 'An rasa rayuka, an kona gidaje a harin da aka kai karamar hukumar Zangon Kataf', ya ce:

"Hukumomin soji da na yan sanda sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna game da hare-hare a wurare biyu, Yagbak da Ungwan Ruhugo a karamar hukumar Zango-Kataf."
"Gwamnatin jihar Kaduna na kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, yayin da ake jiran cikakken rahoto daga rundunar soji, yan sanda da DSS a wuraren biyu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

"Za a sanar da jama'a karin bayani da zaran an tabbatar da wadannan.
"Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da hare-haren, ya roki Allah ya ji kan mamatan, sannan ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar (SEMA) da ta gaggauta zuwa wajen don gani da ido tare da samar da kayan agaji ga garuruwan."

Da aka tuntube shi, ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Mohammad Jalige ba domin bai amsa kiran wayarsa ba.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yan bindigar sun shammaci mazauna kauyukan ne, inda suka ta harbi ba kakkautawa tare da kona gidaje, rahoton Punch.

Barayin da suka sace masu ibada sama da 60 a Kaduna sun bukaci Buhunan shinkafa da jarkan mai

A wani labarin, maharan da suka yi garkuwa da masu aikin ibada 60 a jihar Kaduna sun buƙaci buhunan shinkafa da jarkan man gyada domin ciyar da mutanen.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

Dailytrust ta rahoto yadda yan bindiga suka farmaki cocin Emanuel Baptist dake Kakau Daji, ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna mako ɗaya da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi barazanar cewa matukar ba'a gaggauta kai musu kayan abincin nan ba to zasu bar mutanen cikin yunwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel