Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

  • Gwamnatin jihar Zamfara tana hukunta mutanen da suka saba dokar da Gwamna ya shigo da ita kwanaki
  • Bello Matawalle ya haramta sayen man fetur a cikin robobi, domin a dakile zirga-zirgar ‘yan bindiga
  • An nada kwamiti na musamman wanda yake binciken masu wannan laifi, an kafa kotu na musamman

Zamfara - A ranar Larabar nan gwamnatin jihar Zamfara tace ta hukunta mutane fiye da 1, 000 da suka saba dokar da aka kawo domin a yaki matsalar tsaro.

Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa shugaban kwamitin da aka kafa domin kawo karshen rashin tsaro a jihar Zamfara, Abubakar Dauran, ya bayyana haka.

Abubakar Dauran ya yi wannan bayani ne a yayin da yake gabatar da wani mutumi da aka kama yana sayen man fetur a gidajen mai da-dama a garin Gusau.

Kara karanta wannan

Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi

Zayyanu Bingi ya shiga hannun hukuma

An kama Zayyanu Bingi mai shekara 42 ne bisa zargin yana kai wa ‘yan bindiga man fetur.

Ko da ya musanya zargin, Zayyanu ya shiga hannu a lokacin da yake kokarin dakon man fetur a karo na bakwai, ya boye robobin man ne a cikin wasu buhuna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar dillacin labarai ta rahoto Malam Zayyanu Bingi yana cewa yana sayen man ne domin saidawa mutanen kauyensa da ke da bukatar amfani da fetur.

Gwamnan Zamfara
Gwamna Bello Matawalle Hoto: BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Kwamiti yana bincike na musamman - Dauran.

Shugaban wannan kwamiti na musamman yace ana gudanar da bincike a kan Bingi da sauran wasu da ake zargi da taimakawa ‘yan bindiga da sirrin mutane.

Gwamnatin jihar Zamfara za ta binciki zargin dake kan wuyan wadannan mutane kafin a dauki mataki. Idan an same su da gaskiya, za su gurfana gaban kotu.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

“Gwamnatin jihar Zamfara ta hana sayen fetur da sauran mai a cikin robobi.” - Abubakar Dauran.
“An kama mutane da yawa suna yin irin wannan, suna kai wa ‘yan bindiga man fetur a wuraren da suke buya a cikin jihar nan.”

Dauran yace sun kama mutane 100 da ake zargi da laifin garkuwa da mutane ko taimakawa miyagun ‘yan bindiga a sakamakon hadin-kai da jami’an tsaro.

Labari mai dadi

A ranar Laraba aka ji cewa Dakarun Sojojin sama sun hallaka ‘Yan bindiga yayin suka yi ruwan wuta a wasu kauyukan jihar Kaduna a tsakiyar makon nan.

Gwamnatin Kaduna ta bada sanarwa inda kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da wannan a wani jawabi da ya fitar da yammacin jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel