Barayin da suka sace masu ibada sama da 60 a Kaduna sun bukaci Buhunan shinkafa da jarkan mai

Barayin da suka sace masu ibada sama da 60 a Kaduna sun bukaci Buhunan shinkafa da jarkan mai

  • Maharan da suka sace mutane ana tsaka da Ibada a Kaduna sun bukaci a gaggauta kai musu kayan abinci
  • Rahoto ya bayyana cewa sun nemi buhunan shinkafa, jarkokin man gyaɗa, Maggi, Gishiri da sauransu
  • Shugaban CAN a Kaduna, Hayab, yace yan bindigan sun sara kuɗin fansa da matukar yawa

Kaduna - Maharan da suka yi garkuwa da masu aikin ibada 60 a jihar Kaduna sun buƙaci buhunan shinkafa da jarkan man gyada domin ciyar da mutanen.

Dailytrust ta rahoto yadda yan bindiga suka farmaki cocin Emanuel Baptist dake Kakau Daji, ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna mako ɗaya da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi barazanar cewa matukar ba'a gaggauta kai musu kayan abincin nan ba to zasu bar mutanen cikin yunwa.

Buhunan shinkafa
Barayin da suka sace masu ibada sama da 60 a Kaduna sun bukaci Buhunan shinkafa da jarkan mai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shin maharan sun nemi kudin fansa?

Kara karanta wannan

Aƙalla mutum 7 suka mutu yayin da miyagun yan bindiga suka kai harin farko yankin wannan jihar

Shugaban ƙungiyar kiristoci (CAN) reshen jihar Kaduna, John Hayab, ya shaida wa manema labarai cewa ɓarayin suna neman a basu maƙudan kuɗaɗe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin mutanen ƙauyen wanda yan uwansa na cikin waɗan da aka sace, ya bayyana cewa yan bindigan sun kira waya ranar Alhamis da daddare.

Da yake jawabi da sharaɗin za'a sakaya sunansa, mutumin yace sun bukaci mutanen garin su basu kayayyakin abinci.

Wane irin kayan abinci suka nema?

A jawabinsa yace:

"Mun samu labarin cewa sun kira wayar salula ranar Alhamis da daddare, sun bukaci buhunan shinkafa 5, jarkan man gyada 4, katan din Maggi, da gishiri."
"Sun kuma yi gargaɗin cewa matukar aka ƙi samar musu da abubuwan da suka bukata to zasu bar mutanen da yunwa.

Ya ƙara da cewa ɓarayin sun matsa sosai a kan kayayyakin abincin, wanda suka yi ikirarin cewa mutanen da suka sace za'a ciyar da su.

Kara karanta wannan

Sabon Hari: Duk da dauke sabis, Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Katsina

A cewarsa sun cigaba da nanata cewa idan ba'a kai musu kayan abincin ba, to waɗan da ke hannun su zasu zauna da yunwa.

Yan Napep da yan sanda sun yi arangama

A wani labarin kuma Rikici ya barke tsakanin yan Keke-Napep da jami'an yan sanda, An bindige mutum daya

Wasu na zargin cewa jami'in hukumar yan sanda ne ya daba wa direban Keke-Napep ɗin wuka yayin da wasu ke cewa bindige shi ya yi, kuma ya barshi nan kan hanya har ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin dai tsakanin yan sanda da direbobin Napep ɗin ya faru ne a kan hanyar Command, Meran, Abule-Egba, ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel