Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki kan wasu jami'an 'yan sanda da ke bakin aiki a unguwar Okija da ke yankin Diobu, Port Harcourt, jihar Ribas
  • Maharan sun bindige jami'an 'yan sanda biyu, inda suka mutu a nan take
  • Kakakin ‘yan sandan jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami'ansu sun bi sahun maharan

Port Harcourt, Jihar Ribas - Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wasu jami’an ‘yan sanda biyu da ke aiki a ofishin rundunar na Mile One da ke Diobu, Port Harcourt, jihar Ribas, The Cable ta rahoto.

Wani ganau ya bayyana cewa an bindige jami'an tsaron ne a yayin da suke aikin tsayarwa tare da binciken motoci a unguwar Okija da ke yankin, rahoton Daily Trust.

Read also

'Yan sanda sun yi ram da masu samar da kayan shaye-shaye da barasar bogi mai cutarwa

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas
Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas Hoto: Premium Times
Source: UGC

Shaidan ya ce 'yan bindigar wadanda ke a cikin wata mota, sun afka wa jami’an tsaron da suka mutu sannan suka harbe su bayan sun yi gab da su.

Har ila yau, shaidan wanda yace an yi wa 'yan sandan kautan bauna ne, ya kara da cewa wadanda abin ya rutsa da su sun mutu ne a nan take.

Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rahoton ya nuna cewa tuni jami'an rundunar ‘yan sandan jihar suka bi sahun maharan.

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu

A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta kawo a baya cewa akalla yan sanda hudu ne da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka mutu a ranar Laraba yayin da wasu yan bindiga suka kai hari shingen yan sanda a Obeagu-Amechi a karamar hukumar Enugu ta Kudu.

Read also

‘Yan bindiga sun sa 'yan gari su tara masu kudi nan da Juma’a ko a kawo masu hare-hare

Baya ga jami'an tsaron, mazauna gari da mutane da ke wucewa sun rasu, wasu kuma sun jikkata sakamakon harsashin bindiga yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da yan bindiga.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan sanda sun dakile harin, duk da cewa an rasa mutane a dukkan bangarorin biyu.

Source: Legit.ng

Online view pixel