Bamu yarda da su ba: Amotekun ta kama wasu ƴan arewa 18 cikin trelar wake a Ogun, ta ce su koma inda suka fito

Bamu yarda da su ba: Amotekun ta kama wasu ƴan arewa 18 cikin trelar wake a Ogun, ta ce su koma inda suka fito

  • Jami’an tsaron Amotekun sun kama ‘yan arewa 18 bayan haduwa da tirelar waken da su ka boye a cikin ta tun daga arewacin Najeriya zuwa jihar Ondo a daidai kan titin Arakale da ke babban birnin jihar
  • Kwamandan rundunar, Cheif Adetunji Adeleye ne ya bayyana hakan, inda ya ce da jami’an su ba su ci karo da su ba, da yanzu sun tayar da tarzoma kuma an fara bincike a kan wasu 30 da su ka isa yankin kafin su
  • Adeleye ya ce za su bincike su don jin abinda ya kawo su yankin sannan a mika su ga shugaban hausawan yankin don tabbatar da an mayar da su inda su ka fito

Jihar Ondo - Jami’an tsaron Amotekun sun kama wasu ‘yan arewa 18 bayan cin karo da tirelar da ta dakko su daga arewacin Najeriya zuwa jihar bisa ruwayar TVC News.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige jami'an yan sanda a jihar Ribas

An kama su ne a kan titin Arakale da ke Akure, babban birnin jihar Ondo a wannan makon.

Ba mu yarda da su ba: Amotekun ta kama wata trela dauke da 'yan arewa 18 a Ogun, ta ce su koma inda suka fito
Amotekun ta kama wata trela dauke da 'yan arewa 18 a Ogun, ta ce su koma inda suka fito. Hoto: LIB
Asali: Facebook

LIB ta bayyana yadda shugaban jami’an ya ce ‘yan arewan barazana ne ga tsaron yankin ganin yadda su ke ta kai komo a hedkwatar jami’an da ke Alagbaka a Akure ma abin zargi ne.

Kwamandan rundunar, Cheif Adetunji Adeleye ya bayyana hakan inda ya ce an fara cin karo da ‘yan arewan a babban titin Ilesa-Akure.

Kwamandan ya bayyana yadda su ka shiga garin ta hanyar boyewa a karkashin lodin waken da ke cikin tirelar.

A cewar sa:

“Jami’an mu sun ga tirelar waken wacce ta nufi Akure. Sun tsaya a daidai titin Akure, yayin da ake binciken motar ne aka gano cewa samari guda 18 ne ba wake ba.”

Kara karanta wannan

Borno: ISWAP ta sako manoma 76 da ta kama, ta yi musu bulala kafin sakinsu

Ya ce akwai bukatar su sanar da abinda ya kawo su

Adeleye ya ce wajibi ne matasan su bayyana gaskiyar dalilin da ya sa su ka kwaso kafafun su daga jihohin su zuwa jihar.

Ya kara da cewa za a mika su ga shugaban hausawan yankin don mayar da su daga inda su ka fito. Adeleye ya ce za su iya tayar da tarzoma da ba a dakatar da su ba.

A cewar sa akwai wasu 30 da ake zargin sun riga sun isa garin, kuma za a binciko su don yanzu haka jami’an sun fara neman su.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Kara karanta wannan

Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel