'Yan sanda sun yi ram da masu samar da kayan shaye-shaye da barasar bogi mai cutarwa

'Yan sanda sun yi ram da masu samar da kayan shaye-shaye da barasar bogi mai cutarwa

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke wasu mutane da ke samar da barasa da giya ta bogi a jihar Ribas
  • An kama su da abubuwa da yawa na zargi, ciki har da wasu kwalaben giya da na barasa da yawa
  • A halin yanzu 'yan sanda na ci gaba da bincike, kuma sun ce nan ba da dadewa ba za a mika su kotu

Ribas - Daily Trust ta ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce jami’anta na ‘Puff Adder’ sun kama wata tawagar da ta kware wajen samar da kayan shaye-shaye na jabu a Fatakwal.

SP Nnamdi Omoni, wanda ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a rundunar ‘yan sandan jihar, Fatakwal, a ranar Litinin, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a sansaninsu da ke hanyar Eligbolo a yankin Rumuokoro na Fatakwal.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Rahoton jaridar Punch ya ce an kama su ne a ranar 22 ga watan Oktoba da misalin karfe 3:30 na yamma, kamar yadda Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nnamdi ya bayyana.

'Yan sanda sun yi ram da masu sayarwa mutane barasar bogi mai cutarwa
'Yan sanda sun yi kamen masu sayar da barasar bogi | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Omoni ya ce tawagar ta tsunduma barnar samar da kayan shaye-shaye na jabu da ake kyautata zaton na da illa ga lafiyar al’umma.

Ya ce mutane biyu da ake zargi; An kama Ahayera Collins da Christian John, yayin da wasu suka tsere.

Wasu daga cikin abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin, a cewar Omoni, sun hada da giya iri-iri da barasa da dama da kuma kwalaben da babu komai a ciki da ake jira a cika su da ruwa/kayan shaye-shaye.

Ya ce wadanda ake zargin sun yi bayani mai amfani kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

NAFDAC ta garkame wasu kamfanoni 27 na 'Pure Water' saboda rashin inganci da tsafta

A baya, Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce, duk wani ruwan ledan da bai da lambar NAFDAC, da kyakkyawan rubutu hade da mummunan nahawu wajen rubutu to a sani ruwan bogi ne kuma mara tsafta.

Darakta-Janar na NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta ce tuni hukumar ta rufe kamfanin ruwa guda 27 saboda sun ki bin ka’idojin samar da ruwa mai inganci, inji rahoton BBC Pidgin.

Ta bayyana hakan ne a yayin taron kungiyar masu samar da ruwan leda ta kasa ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel