Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai ba - Mele Kyari ga yan Najeriya

Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai ba - Mele Kyari ga yan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yan kasuwa ke haddasa layin mai da ake gani amma ba tada niyyar kara farashi
  • Shugaban Kamfanin NNPC ya bayyana cewa yanzu haka akwai kimanin litan mai bilyan biyu a kasa
  • Yan kasuwan mai dai tuni sun yi kira ga gwamnati ta dau mataki saboda an kara musu kudi kuma ba zasu dau asara ba

Legas - Kamfanin Man Feturin Najeriya, NNPC, ta kwantarwa da yan Najeriya hankali game da rade-radin tsadar mai yayinda aka fara fuskantar karanci a wasu jihohin Najeriya.

Dirakta Manaja na NNPC, Mele Kyari, ya bayyanawa yan Najeriya cewa su kwantar da hankulansu akwai isasshen man da zai isa ba tare da an sha wahala ba.

Kyari ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a taron manema labaran sashen makamashi na Najeriya NAEC2021, ranar Talata a jihar Legas, rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

A cewarsa:

"Yanzu haka ana rade-radin tsadar mai a kafafen yada labarai amma muna da akalla litan mai bilyan 1.7a kasar nan."
"Hakazalika muna da wani litan mai bilyan 2.3 dake hanyar zuwa saboda babu wani karanci."
"Lallai akwai matsalar kara kudi a wasu defot amma gwamnati ba tada niyyar kara farashin mai."

Ba za'a yi wahalan mai ba - Mele Kyari ga yan Najeriya
Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai ba - Mele Kyari ga yan Najeriya Hoto: NNPC
Asali: Facebook

Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi

Mun kawo muku jiya cewa, kungiyar yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya IPMAN, ta gargadi gwamnatin tarayya cewa da yiwuwan farashin man fetur ya tashi kwanan nan.

Kungiyar tace hakan zai faru ne saboda masu defot sun kara farashi daga wajensu.

Shugaban IPMAN na reshen Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

Ya ce wasu mammalakan defot masu zaman kansu sun kara farashin man daga N148 ga Lita zuwa N153-N155 tun Juma'ar da ta gabata.

Yace kungiyarsu na sanar da gwamnati ne saboda kada a daurawa mambobinta laifi idan suka kara farashin mai saboda ba zasu yarda da asara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel