Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi

Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi

  • Yan kasuwan mai masu zaman kansu sun ce da yiwuwan a fara tsadar mai kwanan nan
  • Sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dau mataki tun da wuri
  • A cewarsu, ba zasu dau asara ba saboda yan defot sun kara farashi

Kano - Kungiyar yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya IPMAN, ta gargadi gwamnatin tarayya cewa da yiwuwan farashin man fetur ya tashi kwanan nan.

Kungiyar tace hakan zai faru ne saboda masu defot sun kara farashi daga wajensu.

Shugaban IPMAN na reshen Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, rahoton Punch.

Ya ce wasu mammalakan defot masu zaman kansu sun kara farashin man daga N148 ga Lita zuwa N153-N155 tun Juma'ar da ta gabata.

Read also

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki

Yace kungiyarsu na sanar da gwamnati ne saboda kada a daurawa mambobinta laifi idan suka kara farashin mai saboda ba zasu yarda da asara ba.

Yace:

"Defot masu zaman kansu na kokarin yiwa gwamnatin tarayya zagon kasa ta hanyar kara farashi duk da cewa gwamnati bata daga farashin litan mai ba."
"Hakazalika muna kira ga shugabannin NNPC suyi bincike kan lamarin saboda masu defot sun kara farashi daga N148 zuwa N153-N155 tun ranar Juma'ar da ta gabata."
"Mun san gwamnatin tarayya kadai ke da hakkin shigo da mai Najeriya."

Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi
Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi
Source: UGC

Ya kara da cewa "yanzu haka, defot dake Warri, Calabar, Legas, da Ogahra a Delta sun kara farashinsu. Muna sa ran NNPC zata yi bincike kan hakan."

Ya tuhumci masu defot din da kokarin haddasa tsadar mai saboda suna ganin karshen shekara ya kusa don su samu dimbin riba.

Read also

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Gwamnatin tarayya ta soke hukumomin man fetur uku, kuma ta sallami shugabanninsu, ga jerinsu

Bayan kafa dokar ma'aikatar man fetur, gwamnatin tarayya ta soke wasu hukumomin ma'aikatar guda uku lokaci guda.

Karamin Ministan arzikin man fetur, Chief Timipre Sylva, ya bayyana hakan ne yayin bikin ranstar da majalisun lura da hakar man fetur na kasa da ruwa a Abuja, ma'aikatar ta bayyana hakan a shafinta na Facebook.

Hukumomin sune:

1. Hukumar arzikin mai (DPR)

2. Asusun lamunin daidaita farashin man fetur (PEF)

3. Hukumar sanya farashi da lura da farashin mai (PPPRA)

Source: Legit

Online view pixel