Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna

Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna

  • Jami'an tsaro sun dirka wa wani mutum dalma a kafa a yayin da ya yi kokarin tseratar da fursuna da suka kawo kotu a Legas.
  • Ana zargin mutum abokin aikin fursunan ne shi yasa ya yi kokarin taimaka masa su tsere tare
  • O.O. Oladokun, mai magana da yawun hukumar gidan gyaran halin ya tabbatar da afkuwar lamarin

Legas - Jami'an hukumar gidajen kula da gyaran hali sun harbi wani mutum a babban kotun jihar Legas da ke Tafawa Balewa Square, TBS.

The Nation ta ruwaito ta ruwaito cewa an harbi mutumin ne a kafarsa yayin da ya yi yunkurin sakin wani fursuna da aka taho da shi kotu.

Da Dumi-Dumi: An harbi wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna
An harbi wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Ana zargin yana daya daga cikin abokan aikin fursunan da aka kawo kotu domin cigaba da sauraron shari'arsa.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

Mai magana da yawun hukumar gidan yarin reshen jihar Legas, O.O. Oladokun ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel