Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

  • Gwamnati na shirin karbawa ma'aikatar ruwa bashin ne a 2022 don samawa yan Najeriya isasshen ruwan sha
  • Wannan na kunshe cikin kasafin kudin 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisa
  • Jihohi bakwai; uku a kudancin Najeriya da kuma hudu a Arewacin kasar zasu amfana da wannan kudi

Abuja - Sakatariyar din-din-din ta ma'aikatar ruwan sha, Mrs Esther Didi Walson-Jack, ta bayyana gaban Kwamitin Mambobin majalisar dattawa kan basussukan gida da waje ranar Laraba.

Mrs Esther ta gurfana gaban Sanatocin ne don bayani kan bukatun basussuka da ma'aikatar ta gabatar a kasafin kudin 2022 da shugaba Buhari ya kai, rahoton Thisday.

Tace gwamnatin zata karbi bashin ne don samar da isasshen ruwan sha ga yan Najeriya a karkara da birane karkashin shirin SURWASH.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa tayi Alla-wadai da shirin karban bashin N290bn don samar da ruwan sha

A bayanin da tayi, tace za'a yi amfani da kudin tsawon shekaru biyar da wannan aiki.

Ta kara da cewa daga cikin kudin, za'a yi amfani da $640 million wajen ainihin aiki yayinda za'a yi amfani da $60 million domin horar da ma'aikata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

za'a N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha
Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha Hoto: Presidency
Asali: UGC

Shugaba Buhari da majalisar zartaswa sun amince a karbi bashin

A riwayar Punch, Sakatariyar ta cigaba da cewa an tattauna lamarin wannan bashi da bankin duniya a Afrilun 2021, kuma majalisar zartaswa FEC karkashin Shugaba Buhari ta amince a karba ranar 11 ga Agusta, 2021.

Wasu jihohi zasu amfana?

Ta lissafa jihohi bakwai da zasu amfana da wannan kudi idan majalisar dattawa ta bada daman karban bashin.

A cewarta, jihohin sun hada da Delta, Ekiti, Gombe, Imo, Kaduna, Katsina, da Plateau

Ta kara da cewa wannan shiri zai samar da ruwa ga makarantu 2,000 da asibitoci, kuma zai taimakawa garuruwa 500 wajen rage yin ba haya a fili.

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

Majalisar dattawa tayi Alla-wadai da shirin karban bashin N290bn don samar da ruwan sha

Kwamitin Mambobin majalisar dattawa kan basussukan gida da waje sun yi watsi da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na karbar bashin $700 million (N290bn) don ma'aikatar ruwa.

Ma'aikatar ruwan za tayi amfani da kudin ne wajen samar da isasshen ruwan sha ga yan Najeriya a karkara da birane karkashin shirin SURWASH.

Mambobin kwamitin majalisar sun bayyana rashin yardarsu da wannan bashi da gwamnatin ke shirin karba

Asali: Legit.ng

Online view pixel