Kotu ta hana Gwamnatin Buhari aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

Kotu ta hana Gwamnatin Buhari aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

  • Gwamnati na shirin karban bashi daga hannun yan Najeriya ba tare da izininsu ba
  • Yanzu Kotu ta ce sam gwamnatin bata isa ba
  • Kungiyar masu hannun jari Palm Wealth ta shigar da gwamnatin Buhari kotu

An haramtawa gwamnatin tarayya aron kudin da mutane suka sa hannun jari dake ajiye a banki bayan karar da aka shigar da ita kotu.

Akwai kudi sama da bilyan 200 dake ajiye a bankuna yanzu haka na mutane wadanda basu waiwaya, kuma gwamnatin shugaba Buhari ta kafa dokar amfani da kudaden matsayin bashi.

Alkali J.O Abdulmalik na babban kotun tarayya dake Abeokuta ya hana gwamnati dabbaka wannan doka kuma ya bayyana cewa kada a yiwa mutane barazana kan kudinsu.

Kungiyar masu hannun jari Palm Wealth ta shigar da gwamnatin Buhari kotu kan wannan abu.

Alkalin ya ce daga yanzu har zuwa lokacin da za'a kammala shari'ar, kada wanda ya gayyaci kamfanoni da mutane da sunayensu ke cikin masu kudi ajiye a banki.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Kotu ta hana Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki
Kotu ta hana Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki
Asali: Facebook

Shin me gwamnati ke nufin yi?

Duk da rashin amincewar masu hannun jari, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba'a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba'a bibiya ba.

Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za'a iya aron kudaden masu hannun jari da ajiyan da mutanen sukayi a banki wanda suka kai shekaru 6 ba'a waiwaya ba.

Gwamnati tace duk kudaden da ba'a bibiya ba za'a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna 'Unclaimed Funds Trust Fund'.

Yanzu gwamnatin na shirin aron wadannan kudaden dake cikin asusun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel