Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki
- Bayan basussukan da gwamnati ta karba daga kasashen waje, an hangi wani sabon asusun da za'a aro kudi
- Bankin duniya, bankin cigaban Afrika, da asusun lamunin duniya na bin Najeriya bashi Biliyoyin dala
- Yanzu gwamnati na shirin karban bashi daga hannun yan Najeriya ba tare da izininsu ba
Duk da rashin amincewar masu hannun jari, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba'a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba'a bibiya ba.
Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.
Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za'a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba'a waiwaya ba.
Gwamnati tace duk kudaden da ba'a bibiya ba za'a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna 'Unclaimed Funds Trust Fund'.
Yanzu gwamnatin na shirin aron wadannan kudaden dake cikin asusun, Thisday ta ruwaito.
"Za'a tura wadannan kudade asusun lamunin kudaden da ba'a bibiya ba kuma gwamnati zata iya karbar bashi daga ciki amma zata biya a duk lokacin da mai hannun jarin ya bukata," dokar ta tanada.
KU KARANTA: Zulum ya warewa mafarauta da CJTF N352m a Jihar Borno
KU KARANTA: Minista ya umarci NERC ta fadawa DisCos a dakatar da karin kudin wuta
A wani labarin daban, ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe naira biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe N135.6 miliyan a kan lemuka kamar yadda jaridar The Cable ta gani a kasafin kudi.
A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021.
A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng